Nazari daga Katsina Times
Marigayi Galadiman Katsina, Mai Shari’a Mamman Nasir (Allah ya jikansa da rahama), shi ne ya jagoranci sake gina Kofar Soro, kamar yadda ya bayyana a wata hira da ya yi da Taskar Labarai a shekarar 2014, dangane da tarihin rayuwarsa.
A cikin hirar, Marigayi Mamman Nasir ya ce, sun tsara yadda za a gyara gaban kofar domin ya zama wajen hutuwa ga jama'a a kowane lokaci. Wannan mataki, a cewarsa, yana kara nuna martabar gidan Sarki da kuma karfafa alakar jama'a da masarauta. Sama da shekaru 50, gaban kofar Soro ya kasance wajen taruwa da hutu ga al'umma.
Sai dai a sabon gyaran da aka yi a shekarar 2024, an killace wajen da ake zama da waya, an kuma rufe shi da kwaɗo. Wannan mataki ya jawo cece-kuce daga jama’a, musamman a bayan fage, inda da dama ke ganin ba a yi nazari mai zurfi ba kafin daukar wannan mataki, kuma ba a tuntubi jama’a ba.
Wurin yana kan hanya mai yawan zirga-zirgar jama’a, wanda ke hade da asibiti, kasuwa, tashar mota ta Kofar Sauri, da makarantu. A yanzu ana ganin wajen za a rika bude shi sau biyu ne kacal a shekara — yayin Babbar Sallah da Karamar Sallah.
A sake duba wannan mataki, tare da nazarin amfanin bude wajen da kuma illar rufe shi, kafin yanke hukunci da ya fi dacewa da maslahar al’umma.