Gwamnan Jihar Kebbi, Malam Nasir Idris, Kauran Gwandu, a yau talata 1 ga watan Afrilu 2025, ya jagoranci wata tawaga don kai ta'aziyya ga Gwamna Dikko Umaru Radda bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Barebari, wadda ta rasu tana da shekaru 93.
A cikin sakon ta’aziyyarsa, Gwamna Idris ya bayyana marigayiyar a matsayin mace wadda rayuwarta ta kasance cike da albarka da rahamar Ubangiji.
"A yau muna hallara da zuciya mai cike da alhini don neman rahama da gafara ga mahaifiyarka—wacce ita ma tamu ce—wadda ta koma ga Mahaliccinta. Shekarunta 93 shaida ce ta rayuwa mai albarka. A al’adar Hausawa, muna cewa: 'Mutum ya yi rabo idan ya bar duniya lafiya, ya bar baya da kyakkyawar gado ta soyayya da hadin kai.' Rayuwarta mai tsawo da cike da kima wata babbar ni’ima ce," in ji Gwamna Idris.
Gwamnan Kebbi ya bayyana cewa ya samu labarin rasuwar ne a yayin da yake gudanar da ibadar Umrah a Makka. Ya ce, "Lokacin da muka samu labarin a Makka, zukatanmu sun haɗu da naku a addu’a. Yayin da muke gudanar da Umrah, muna tare da ku a cikin alhini, muna daure da juna bisa imani da ‘yan’uwantaka. Yanzu da muka dawo, mun zo tare da iyali da mutanenmu don mu nuna goyon bayanmu a fili."
"Munga yadda kuka tsaya a tare da ita a lokutanta na ƙarshe—kana rike da hannunta, kana gefenta. Wannan ba karamin daraja ba ne, domin yana tunatar da mu cewa akwai girmamawa da falala wajen kula da iyayenmu har zuwa mintuna na ƙarshe. Wannan yana ƙarfafa mu da mu ci gaba da girmama zumuncinmu a wannan duniya da ke wucewa," in ji shi.
A ƙarshe, Gwamna Idris ya yi addu’a da cewa, "Allah Madaukakin Sarki ya gafarta mata, ya lullube ta da rahamarSa, ya kuma sanyata a cikin matsuguni mafi girma—Jannatul Firdaus. A gare ku duka da iyalanku da duk waɗanda suka yi soyayya da ita, muna rokon Allah Ya ba ku haƙuri da juriya. Allah Ya sa rayuwarta ta zama abin koyi ga mu gaba ɗaya."
Da yake mayar da martani a madadin Gwamna Radda, Mataimakin Gwamna Faruk Lawal Jobe ya nuna godiya da jinjina ga wannan ziyara ta ta’aziyya.
"Wannan taro, duk da cewa yana da nasaba da bakin ciki, yana tunatar da mu ƙarfin haɗin kai. Kun zo ba kawai da jami’an gwamnatinku ba, har da iyalinku don yin alhini bisa rasuwar mahaifiyarmu—mahaifiyar Gwamna Dikko Radda. Wannan alama ce ta ƙauna da jin kai, kuma muna matuƙar godiya," in ji Mataimakin Gwamna.
Ya ƙara da cewa, "A madadin iyalan Gwamna Dikko Radda, Gwamnatin Jihar Katsina, da al’ummar jihar baki ɗaya, muna mika godiya mai zurfi. Allah Ya karɓi wannan kyautayyar taku a matsayin aikin lada, Ya kuma ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin jiharmu da taku."
Gwamna Idris ya samu rakiyar wasu daga cikin iyalansa da manyan jami’an gwamnati daga Jihar Kebbi.
'