Kisan Gillar Sojoji A Ranar Kudus A Abuja: Gaskiyar Abin Da Ya Faru Da Mu – Harkar Musulunci

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29032025_183916_IMG-20250329-WA0209.jpg

Daga Zainab Rauf, Abuja

Dandalin Resource Forum na Harkar Musulunci ta yi Allah wadai da harin da rundunar sojojin Nijeriya (Guard Brigade) ta kai kan masu muzaharar ranar Kudus ta duniya ta 2025 a birnin Tarayya Abuja. Harin, wanda ya auku a ranar Juma’a, 28 ga watan Maris, ya haifar da asarar rayuka da kuma raunuka da kuma kama daruruwan masu muzaharar.

Harkar Musulunci ta yi wannan Allah wadai din ne a yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja a yau Asabar. A cikin wata sanarwa da Farfesa Abdullahi Danladi ya sanyawa hannu, Harkar musulunci ta bayyana cewa: “Muna yin Allah wadai da harin da Guard Brigade ta kai kan masu muzaharar ranar Kudus ta duniya ta 2025 a Abuja.”

A cewar sanarwar, “a jiya, 28 ga Maris 2025, wanda ya kasance Juma’ar karshe na watan Ramadan 1446H, ya kasance ranar Kudus ta duniya, rana da Imam Khomeini (QS) ya ware domin nuna goyon baya ga wadanda ake zalunta a duniya, musamman Falasdinawa. Ana gudanar da muzaharar ranar Kudus a kasashe daban-daban kamar Biritaniya, Faransa, Amurka, Jamus, Ostiraliya, Sweden, Kanada da kuma kasashe da dama a Asiya, Afirka, Latin Amurka da Gabas Ta Tsakiya.”

“Harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky tana gudanar da muzaharar ranar Kudus ta duniya sama da shekaru 40 a Nijeriya. Sai dai a bana, an gudanar da muzaharar cikin lumana a duk fadin Nijeriya, sai dai Abuja kadai aka afka mata.”

Sanarwar ta bayyana yadda muzaharar ta fara: “An fara muzaharar ranar Kudus ta duniya ta 2025 a Abuja cikin kwanciyar hankali daga Masallacin Usman Bin Affan da ke kan titin Aminu Kano Crescent, Wuse 2, Abuja. Bayan ƴan mintuna da fara muzaharar, sai wasu dakarun Sojojin Nijeriya (Guard Brigade) suka kawo hari, suka yi amfani da harsasai masu rai. Mutane da dama sun ji munanan raunuka daga harbin bindiga, wasu kuma sun rasa rayukansu sakamakon wannan zalunci. Baya ga kashe masu muzahara da ba su da makamai, sojojin sun kuma aikata munanan abubuwa kamar cafke mata a cikin harabar masallacin Usman Bin Affan, dukan mata da yara, cire hijabi daga jikinsu a wajen masallacin; wadannan ayyukan laifi ne a addinin Musulunci da dabi’un Musulmi.”

Sanarwar ta karyata rahotannin da ke cewa an yi artabu: “Ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito ba cewa an yi artabu, babu wani abu da masu muzahara suka aikata da zai haifar da wannan zalunci. Hakika, masu muzaharar Kudus, wadanda suka hada da maza, mata da yara, Musulmi da Kiristoci, suna tafiya cikin lumana daga masallacin bayan sallatar Jumu’a inda suka nufi kasuwar Wuse, kwatsam sai sojojin suka tare su da wata motar yaki sannan suka fara bude wuta kan masu muzaharar, da dama daga cikinsu mata da yara ne.”

Sanarwar ta kara da cewa: “A ranar 27 ga Maris 2025, wata wasika daga ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (NSA) da ta bayyana a shafukan sada zumunta, tana umartar jami’an tsaro da su dauki matakin da ya dace kan muzaharar Kudus Ta Duniya da za a gudanar. Wasikar mai lamba NSA/366/S, wadda aka aikawa dukkan hukumomin tsaro, ta bayyana cewa ‘akwai bayani cewa Harkar Musulunci ta shirya gudanar da muzahara a ranar Juma’a, 28 ga Maris, 2025 a jihar Nasarawa da Abuja don nuna goyon baya ga Falasdinu.’ Wasikar ta kara da cewa ‘An bukaci a dauki matakin da ya dace kan lamarin.’”

Harkar Musulunci ta bayyana cewa an shirya wannan hari tun farko dama: “Tun bayan bayyanar wannan wasika, jami’an tsaro, musamman a Abuja, sun shirya don aikata wadannan laifuka a harabar Masallacin Usman Bin Affan. Wannan za a iya gani daga yadda aka jibge jami’an tsaro a Masallacin Kasa na Abuja da wasu masallatai a cikin birnin.”

Harkar Musulunci ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana da munafunci a manufofinta na hulda kasashen waje: “Abin mamaki ne yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke nuna sabani a manufofinta. A yayin da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tugar, ke cewa a cikin wata hira da Al-Jazeera a birnin Doha, a Qatar a watan Maris 2025 cewa ‘Isra’ila dole ta dakatar da yakin da take yi a Gaza, kuma duniya ta daina nuna son kai kan kisan gillar da ake yi a yankin,’ sai kuma NSA ke bayar da umarnin kai hari kan masu muzaharar ‘Free Palestine’ a Abuja.”

Game da adadin mutanen da aka kashe da wadanda aka kama kuwa, sanarwar ta bayyana cewa: “Bayanan da aka tabbatar sun nuna cewa Guard Brigade da ƴan sanda sun cafke mutane 380, ciki har da mata da yara, a yayin da mutane hudu aka tabbatar sun rasa rayukansu. Wadanda aka kama suna tsare a SARS Abbator, Guzape, Abuja. Wadanda aka kashe kuwa sun hada da Shaheed Ibraheem Dalhat (Sharif Albani), Shaheed Nasir Abubakar, Shaheed Abdulaziz Abubakar, da Shaheed Auwal Abbas Bichi. Duk da haka, jami’an tsaro na boye wasu gawarwakin da yawa na mutanen da suka kashe wanda bai gama bayyana ba. Za mu ci gaba da sanar da al’umma kan sabbin bayanai da suka shigo.”

Harkar musulunci ta dora alhakin wannan hari kan shugaban kasa: “Muna dora alhakin wannan kisan kai da cin zarafi ga addinin Musulunci da dabi’un musulmi ga Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ba da dama ga Guard Brigade su aikata wadannan ta’asa yayin harin da suka kai a Masallacin Usman Bin Affan, Abuja.”

Sanarwar ta karkare da cewa: “A bisa haka, muna bukatar a saki duk wadanda aka kama ba tare da wani sharadi ba dangane da muzaharar Ranar Kudus Ta Duniya da aka gudanar a Abuja a ranar 28 ga Maris, 2025. Haka kuma, muna bukatar a hukunta duk masu hannu a kashe-kashen da aka yi wa masu muzaharar ‘Free Palestine’.”

Follow Us