Bashin Naira 650,000: An cakusa Tsakanin Kwamishinan Gona Da Chairman Na Bakori

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17032025_161742_IMG-20250317-WA0138.jpg

@ Katsina Times 

A makon da ya gabata ne aka kai ruwa rana da nuna wa juna yatsa tsakanin Kwamishinan Gona na jihar Katsina, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori da Shugaban ƙaramar hukumar Bakori, a jihar Katsina, Hon. Ali Mamman Mai Chitta, a kan wasu kuɗaɗe Naira 650,000.

Abin da ya faru shi ne, an zo rabon kayan abinci wanda gwamnatin Katsina ta bayar a riƙa ciyarwa a ko'ina a faɗin jihar Katsina, a zango na biyu na rabon waɗannan kayan abincin, sai Farfesa Bakori ya yi ƙorafin cewa yana bin ƙaramar hukumar bashin kuɗi tun Ramadan ɗin bara (2024), amma ba a biya shi ba.

Wani da aka yi lamarin gabansa ya faɗa mana cewa, Farfesan ya tashi tsaye yana faɗa, tare jadadda cewa dole sai an biya shi kuɗinsa da yake bi.

Waɗanda ke wurin baki ɗaya ba wanda ya goyi bayansa. Suna ta ba shi haƙuri suna cewa a siyasa tunda hidimta wa al'umma aka yi, ya kamata ya kashe nasa kuɗin, amma ya ƙi sauraren kowa, sai da ta kai shugaban ƙaramar hukumar Hon. Ali Mamman Mai Chitta ma ya ga cewa sai ya bi ta tsiya za a zauna lafiya. Da shi ma ya yi sama, sai aka cimma matsaya, inda Farfesa Bakori ya yi haƙuri zuwa Litinin mai zuwa za a biya shi kuɗaɗensa.

A wajen kamar yadda ganau ya tabbatar mana, sai da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Mai Chitta, ya ba shi haƙuri, ya ce ba su da kuɗi, kuma suna da basussuka da yawa a kan su, suna ta ƙoƙarin biyan kowa kafin a rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa.

YA ASALIN BASHIN YAKE?

Mun tambayi wani daga ƙaramar hukumar wanda ya san duk abin da ya faru, inda ya faɗa mana cewa, a Ramadan ɗin bara (2024) aka ba ƙaramar hukumar Bakori kayan abincin da za a raba wa mutane kyauta, shi Kwamishinan Gona shi ne ya kawo kayan daga Katsina.

Sai ya nemi a mayar masa da kuɗin da ya kashe wajen kawo kayan daga Katsina zuwa Bakori Naira 650,000.

Mai ba mu labarin ya ce, sai Shugaban ƙaramar hukumar ya dage a kan jiha ce za ta biya ba ƙaramar hukuma ba. 

Daga baya sai Kwamishina Bakori ya ce, lallai ya samo tabbacin ƙaramar hukuma ce za ta biya. Don haka a biya shi kuɗinsa.

A nan ne shugaban ƙaramar hukumar ya sha alwashin zai biya kuɗaɗen in sun sami kuɗi.

Wannan ne ya kai har Ramadan ɗin bana 2025, inda da aka zo za a raba kayan wannan shekarar kashi na biyu ya ta da balli.

Majiyarmu ta samu tabbacin ƙaramar hukumar ta tabbatar za ta biya shi kuɗinsa a ranar Litinin 17/3/2025.

Mun yi kokarin jin ta bakin Shugaban ƙaramar hukumar, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba. Duk wayoyinsa ba sa shiga.

Jaridun Katsina Times sun tuntuɓi Kwamishinan Gona, Farfesa Bakori don jin gaskiyar abin da ya faru, inda ya tabbatar mana cewa lamarin ya faru, kuma a gaban wasu da ake cikin mitin da su.

Ya ce amma maganar ta gida ce (personal) ce. Ya ce, "Chairman ɗin ƙani na ne, kuma ɗan'uwa ne. Don haka na jawo hankalinsa a kan yadda ake kuka da shi. Har na  ba shi misali da ni ma tun bara ina bin kuɗi, amma ba a biya ni ba."

Farfesa Bakori ya ce, "Na yi maganar ne don Shugaban ƙaramar hukumar ya gyara wasu dabi'unsa da jama'a ke kuka da su.

Farfesa ya tabbatar cewa, an ba shi tabbacin za a biya shi zuwa yau Litinin 17/3/2025.

Katsina Times 
@ www.katsinatimes.com

Follow Us