Binciken Katsina Times Akan Kamfanin Jiragen Sama na United Nigeria da Zai Fara Jigila Daga Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11032025_070124_FB_IMG_1741676322744.jpg


@Katsina Times
www.katsinatimes.com

An kaddamar da kamfanin jiragen sama na United Nigeria Airline yau a filin jirgin saman Katsina. Kamfanin, wanda aka kafa a shekarar 2020, ya samu lasisin fara aiki a 2021. Mallakar wani dan jihar Enugu ne, kuma hedkwatarsa tana filin jirgin sama na jihar Enugu.

Kamfanin yana da jirage guda shida, amma an dakatar da hudu daga tashi. Duk zirga-zirgarsa na tsakanin Legas, Abuja, da wasu jihohin Kudu maso Gabas. An ba shi damar fara jigila zuwa Sokoto, amma har yanzu ba a fara ba.

A kwanakin baya, an dakatar da kamfanin daga aiki bayan daya daga cikin jiragensa ya zarce cikin ciyawa yayin sauka a filin jirgin Legas, maimakon ya tsaya a inda ya dace. Sai dai babu asarar rai ko jikkata a wannan hadari.

Binciken Katsina Times ya tabbatar da cewa United Nigeria Airline shine kamfanin jiragen sama da ke da mafi karancin jari a cikin dukkan kamfanonin jiragen sama na Najeriya. Hakazalika, binciken ya nuna kamfanin na fama da basussuka da yake kokarin biya.

Dangane da ma'aikatansa, an tabbatar da cewa sun samu horo, amma ba cikakke ba saboda matsalar kudi. Har ma ana zargin cewa albashin ma’aikatan, ciki har da matukan jirgi, bai kai na sauran kamfanonin jiragen sama ba.

Duk da cewa hukumomi sun ba da izinin cewa jiragen United Nigeria Airline na iya tashi da yin jigila, wasu fasinjoji daga jihar Bayelsa na bayyana damuwa kan lafiyar jiragen. Wasu ma suna bayyana cewa kafin shiga jiragen, sai sun yi addu’a tare da rike littafin Baibul, kamar yadda a Musulunci ake shiga da alwala.

Katsina Times

Jaridar Taskar Labarai

Samun Labarai Cikin Sauri a Dukkan Manhajojin Sada Zumunta

07043777779 | 0805777762

Follow Us