MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada cewa dole ne addini, siyasa, da mulki su tafi tare domin gina makomar Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Kaduna yayin da yake jawabi a taron Laccar Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), da Muryar Nijeriya (VON) suka shirya.
Taron, wanda ke da taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shiga Malaman Addini Siyasa da Tasirin sa,” ya ba da damar tattaunawa kan rawar da shugabannin addini suke takawa a harkokin mulki.
Idris ya ce: “Ina da yaƙinin cewa wannan jerin bitoci za su ci gaba da haifar da sauyi mai kyau a ƙasar mu.
“A cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda iyalai ke taruwa don yin addu’o'i, nazari, haɗin kai, da tausayin juna, tasirin abubuwan da ke cikin jigon yau—wato addini, siyasa, da mulki—yana da alaƙa da jiya, yau, da gobe. Babu shakka, wannan abu ne da dole mu ci gaba da fahimtar shi da sarrafa shi.
“Amma yayin da muke tafiya a cikin waɗannan al’amura, muna fuskantar sauye-sauyen siyasa na cikin gida da na waje da ke shafar fahimtar mu kan haɗin kan ƙasa.”
Ministan ya yaba da halartar manyan baƙi a wajen taron, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani; da Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Malam Idi Mukhtar Maiha, da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, wanda shi ne uban taron.
Haka nan, ya jinjina wa fitattun malamai irin su Sheikh Morufu Onike Abdulazeez da Farfesa Isma'ila Shehu, yana mai cewa gudunmawar su tana da matuƙar muhimmanci.
Idris ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan wata mai alfarma na Ramadan don yin nazari, haɗin kai, da sabunta aniyar su ta cigaban ƙasa.
Ya kuma jaddada nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta samu, musamman amincewa da kasafin kuɗi na naira tiriliyan 54, wanda ya mayar da hankali kan ɓangarori masu muhimmanci kamar tsaro, ilimi, ababen more rayuwa, kiwon lafiya, da noma.
Ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa bisa ƙirƙiro Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi, yana mai bayyana hakan a matsayin wata babbar manufa da za ta kawo cigaba ga tattalin arziki da zaman lafiya a ƙasa.
“Yayin da muke tafiya a cikin harkokin siyasa da mulki, da tasirin su kan yanke shawara, yana da matuƙar muhimmanci mu riƙa yin zaɓi nagari,” inji shi.
Ministan ya kammala da yin kira ga ‘yan ƙasa da su rungumi ɗabi’un ƙauna, tausayi, da juriya a lokacin watan Ramadan da bayan sa.
“Allah ya albarkaci iyalan mu, ya shiryar da mu, ya kuma ba mu hikima a dukkan al’amuran mu. Ramadan Kareem,” in ji shi.
AlMizan