Hon. Aminu Balele Kurfi Ya Gina Sabbin Masallatai Biyu a Kurfi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23022025_191604_IMG-20250223-WA0120.jpg


Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Dutsin-ma da Kurfi, Hon. Aminu Balele Kurfi (Ɗan Arewa), ya kammala gina sabbin masallatai guda biyu a Ƙaramar Hukumar Kurfi tare da miƙa su ga al’umma.

Bikin buɗe masallatan ya fara ne da na unguwar Kofa, wanda Hon. Balele ya damƙa wa ƙungiyar Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah (IZALA) ta hannun shugabanta, Malam Garba Abdulkarim.

Haka nan, an buɗe masallaci na biyu da ke Mankara Huta, wanda aka miƙa ga ƙungiyar Munazzamatul Fityanul Islam (DARIQA) ta hannun shugaban ta, Malam Iyal Kofar Arewa.

Taron ya samu halartar manyan malamai, jiga-jigan ‘yan siyasa da sauran al’ummar yankin, waɗanda suka nuna farin ciki da wannan ci gaban.

A ƙarshe, an gudanar da addu’o’in zaman lafiya da ci gaban ƙasa, tare da roƙon Allah (SWT) da ya saka wa Hon. Aminu Balele Kurfi da alheri.

Follow Us