Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025
Sashen Kula da Lafiya na Harkar Musulunci a Najeriya (ISMA) ya shirya taron fadakarwa don ilmantar da al’ummar musulmi kan yadda za su kula da lafiyarsu yayin azumin Ramadan. Taron, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025, a unguwar Daki-Tara, Jihar Katsina, ya gudana ne a karkashin jagorancin shugaban sashen na jihar, Malam Abdulkarim Husamatu. Taron ya mayar da hankali kan abinci mai gina jiki da ya dace da mai azumi da kuma irin nau’in da ya kamata a guje wa don kiyaye lafiya.
Masana a fannin lafiya sun gabatar da jawaban ilimantarwa a taron. Jami’in Tuntuba na UNICEF Nigeria, Alhaji Umar Ahmed, ya gabatar da kasida mai taken “Nau’o’in Abinci Mai Gina Jiki da Suka Dace da Mai Azumi,” inda ya bayyana irin abincin da ke taimakawa wajen samar da kuzari da kuma kare lafiya yayin azumi.
Haka kuma, Malam Kabir ISMA ya gabatar da bayani mai taken “Irin Abincin da Ya Kamata Mai Azumi Ya Kaucewa,” inda ya ja hankalin jama’a kan illar cin abinci mai yawan mai da sukari, wanda ke haddasa matsaloli kamar hauhawar jini da kiba.
Farfesa Abdullahi Danladi daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ya yi cikakken bayani kan yadda halin tattalin arziki ke shafar zabi da ingancin abinci yayin azumi. Ya bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi don kiyaye lafiyar jiki da inganta abinci mai gina jiki duk da yanayin tattalin arziki.
Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Yaqub Yahaya Katsina, ya rufe taron da jawabi mai taken “Tasirin Azumi ga Lafiyar Jiki da Ruhi.” Ya jaddada cewa azumi ba kawai ibada ba ce, har ila yau yana da muhimmiyar rawa wajen tsaftace jiki da karfafa tunani da ruhi.
Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba, ya nuna damuwa kan matsalar talauci da ke addabar al’umma, tare da yin addu’ar samun sauyi mai dorewa.
Taron ya samu halartar manyan baki da suka hada da Sheikh Isma’il Zakariyya Alkashnawi, PhD, Sarkin Fawan Katsina, Alhaji Nura, wakilan Red Cross, Jama’atu Nasrul Islam, da kungiyoyin agaji daban-daban.
Mahalarta taron sun bayyana gamsuwa da shawarwarin da aka bayar, tare da yin kira ga ci gaba da shirya irin wannan taruka don fadakar da al’umma kan muhimmancin kula da lafiya yayin azumin Ramadan.