Katsina F.A. Ta Shirya Tsaf Don Gudanar da Zabe a Jihar
Kungiyar Kwallon Kafa ta Jihar Katsina (F.A.) ta bayyana shirinta na gudanar da zabe domin ci gaban wasanni a jihar.
Mataimakin Shugaban Kungiyar, Umar Inta Mai’adua, ya bayyana hakan bayan korafe-korafen da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa suka gabatar.
Ya bayyana cewa rashin tsaro a sassa daban-daban na jihar ne ya hana gudanar da zaben a baya, amma yanzu dukkan shirye-shirye sun kammala domin gudanar da zaben a lokacin da ya dace.
Mai’adua ya kuma yi karin bayani kan mukamin mataimakin sakatare na kungiyar, wanda shugabancin jihar ya samar, yana mai cewa hukumar kwallon kafa ta kasa ta amince da kafa wannan matsayi.
Daga karshe, ya yi kira ga masu sukar shugabancin kungiyar da su kara hakuri, yana mai tabbatar da cewa dukkan abubuwa za su daidaita nan ba da jimawa ba.
Fans
Fans
Fans
Fans