Dalibai 373 a Aji Guda: Barazana Ga Lafiya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17022025_144012_IMG-20250217-WA0012.jpg

Dalibai 373 a Aji Guda: Barazana Ga Lafiya

Wani bincike da daliban kiwon lafiya suka gudanar a makarantar firamare ta gwamnati da ke Kwado ya bayyana yadda cunkoso a ajujuwa ke haifar da hadari ga lafiyar dalibai. Daliban, waɗanda ke karatu a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Cognate College of Health Sciences, sun gudanar da rangadi a makarantar a ranar 17 ga Fabrairu, 2025, domin wayar da kan ɗalibai kan tsaftar jiki da muhalli (Personal Hygiene).

Cunkoso a Ajujuwa: Babbar Barazana

A yayin rangadin, daliban sun gano cewa a wasu azuzuwa, yawan ɗalibai na haura 370, lamarin da ke iya haddasa yaduwar cututtuka musamman a irin wannan lokaci na zafi. Sun bayyana cewa rashin wadatattun ajujuwa da wuraren wanke hannu na daga cikin matsalolin da ke barazana ga lafiyar ɗaliban makarantar.

Daliban sun gabatar da wasu shawarwari ga mahukuntan makarantar, da suka haɗa da:

  • Samar da rijiyar burtsatse (borehole) don inganta tsaftar ruwan sha.
  • Kariya daga cunkoso ta hanyar ƙarin ajujuwa.
  • Gina karin bayan gida (toilets) domin rage cunkoso a wuraren buƙata.
  • Kula da abincin da ake sayarwa a filin taron dalibai don guje wa cututtuka masu nasaba da abinci mara tsafta.

Martanin Hukumar Makaranta

Shugaban aikin (Project Coordinator) na makarantar, Malam Faruk Mahuta, ya bayyana cewa matsalolin da aka lissafa ba sabbi ba ne, domin tuni sun sha gabatar da koke ga hukumomin da abin ya shafa, amma har yanzu ba a ɗauki matakin da ya dace ba. Ya yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umar Radda, da ya duba halin da makarantar ke ciki domin kawo ɗauki.

Godiya da Taimako

A ƙarshe, daliban kiwon lafiya sun raba kyaututtuka kamar sabulu da omo domin tallafa wa daliban wajen tsaftar jiki. Malaman makarantar da daliban da suka halarci taron sun nuna farin cikinsu da yadda aka karɓe su tare da fatan cewa matsalolin makarantar za su samu magani.

Usman Ayuba MASANAWA
Danmasani Radio

Follow Us