Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Yayin da zaben kananan hukumomi a Jihar Katsina ke kara karatowa, dan takarar jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Katsina, Honorable Isah Miqdad AD Saude, ya ci gaba da yakin neman zabensa a ranar Talata, 11 ga watan Fabrairu. Ya ziyarci mazabun Yamma I, Yamma II da Kudu I, duka a cikin garin Katsina, domin ganawa da al’umma, matasa, dattawa da masu ruwa da tsaki a siyasa.
Dubban jama’a ne suka taru domin tarbar dan takarar tare da nuna goyon baya, fatan alheri da yin addu’ar samun nasara. Yakin neman zabensa ya jawo hankalin jama’a daga sassa daban-daban, ciki har da matasa, mata da manyan ‘yan siyasa masu fada a ji.
Taron ya samu halartar fitattun ‘yan siyasa da dattawan yankin, wadanda suka yi jawabi tare da bayyana goyon bayansu ga dan takarar. Daga cikin su akwai Alhaji Iro Teacher, tsohon mashawarci ga gwamnatin Aminu Masari; Alhaji Lolo Dakare; Alhaji Yusuf Barmo; da Alhaji Musa Yusuf Gafai, tsohon dan takarar majalisar tarayya kuma shugaban kungiyar Dikko Project Movement. Sauran sun hada da Abubakar Musa (kansila), Bala Mafiya, Shehu Abba, Yusuf Jibril, Abubakar Usman Sarki, Babangida Nasamu (tsohon dan majalisar dokokin jihar Katsina), Malam Ali Kaura da sauran jiga-jigan siyasa.
A jawabin da ya gabatar, Hon. Isah Miqdad AD Saude ya bayyana cewa zai mayar da hankali kan ci gaban matasa, mata da nakasassu, inda ya sha alwashin samar musu da damammakin ilimi, ayyukan yi da ingantaccen rayuwa. Ya tabbatar wa al’umma cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga jin dadin talakawa da ci gaban yankin.
Yayin da zaben ke kara karatowa, yakin neman zabensa na ci gaba da samun karbuwa, inda jama’a ke nuna goyon bayansu da fatan nasara ga dan takarar APC a Karamar Hukumar Katsina.