Gwamnatin Tarayya Ta Sake Baiwa Kamfanin da babu, kwantaragin Hanyar Abuja-Kaduna
- Katsina City News
- 21 Jan, 2025
- 56
Gwamnatin Tarayya ta sake baiwa kamfani mai suna Messers Infoquest Nigeria Limited kwangilar aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna, duk da cewa rahotanni sun nuna cewa kamfanin baya Aiki, A shafin Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC). Wannan mataki ya jawo tambayoyi game da halaccin shari’a da dabi’ar kwangilar, kasancewar dokar CAMA 2020 ta hana bayar da kwangila ga kamfanonin da ba sa aiki.
Hukumar Kula da Siyasar Kwangiloli ta Kasa (BPP) ta bayar da Takardar Rashin Wani Jayayya kan kwangilar, wadda dokar Public Procurement Act 2007 ta amince da ita. Wannan takardar tana tabbatar da cewa tsarin siyan kayan aikin ya bi ka’idojin doka, tana ba wa ma’aikata damar ci gaba da bayar da kwangilar da kuma biyan kudade.
Sai dai, matsayi na kamfanin Infoquest Nigeria Limited a shafin CAC ya nuna cewa kamfanin ba ya aiki, wanda ke nufin ya gaza cika wajibai na doka kamar bayar da rahotannin shekara-shekara.
A cewar dokar CAMA 2020, kamfanonin da ba sa aiki ba su da izinin shari’a na aiwatar da kwangiloli ko yin kasuwanci. Sashe na 525(3) da 526 na dokar ya baiwa CAC damar cire irin wadannan kamfanonin daga rajistarsu, wanda hakan ke nufin sun daina wanzuwa a matsayin halaltattun kamfanoni.
Rahotanni sun kara nuna cewa Infoquest Nigeria Limited, wanda aka yi rajista a ranar 16 ga Yuni, 1997, tare da lamba RC 315362, yana da jarin kasa da N100,000 kacal, kuma ba a taba samun rahoton da ya biya wajibai na shekara-shekara ba.
Rashin Wanzuwa a Zahiri da Intanet
Wakilan jaridar Daily Trust sun ziyarci adireshin kamfanin da aka nuna a shafin CAC, wato 39 Falohun Street, Orile, Lagos, amma babu wata shaida da ke nuna cewa kamfani na aiki a wurin. Mazauna unguwar sun tabbatar da cewa babu wani ofishin kamfani mai suna Infoquest Nigeria Limited a wurin. Bugu da kari, kamfanin baya da wata shaida a kafafen intanet, wanda hakan ya kara tambayoyi kan cancantar kamfanin wajen gudanar da wannan aikin mai tsada sosai.
Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana cewa Infoquest Nigeria Limited ya samu wannan kwangilar ne daga cikin kamfanoni shida da suka nuna sha’awar aikin, ciki har da manyan kamfanoni kamar Julius Berger Nigeria Plc da Hitech Construction Company Limited. Duk da haka, Daraktan Watsa Labarai na ma’aikatar, Mohammed A. Ahmed, ya bayyana cewa ministan bai tabbatar da bayar da kwangilar ba, illa dai ya bayyana samun wata takarda daga hukumar BPP.
Shugaban Hukumar BPP, Dokta Adebowale Adedokun, ya tabbatar da samun korafe-korafe kan batun kamfanin, amma ya kare bayar da Takardar Rashin Jayayya. Ya ce kamfanin ya cika dukkan sharuɗɗan da ake bukata, ba tare da wani tasirin siyasa ba. Ya kuma bayyana cewa kamfanin yana da tarihin gudanar da manyan ayyuka, ciki har da kwangiloli daga FCDA da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.
Duk da bayanan BPP, rashin bayyananniyar shaida kan matsayin Infoquest Nigeria Limited ya ci gaba da haifar da tambayoyi. Masu ruwa da tsaki sun bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da sahihancin tsarin kwangilar, tare da ganin cewa an bi dokoki da ka’idojin da suka dace.
Wannan rikici ya sake bayyana bukatar bin diddigi da tabbatar da gaskiya a tsarin siyan kayan aikin gwamnati a Najeriya, musamman wajen bayar da kwangiloli ga kamfanoni da ba su cika sharuddan doka ba.