Kungiyar Amnesty International Ta yi kira ga Daukar matakan gaggawa akan hare-haren jiragen sama Sokoto

top-news

Kungiyar kare hakkin dan’adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gudanar da bincike kan hare-haren sama da suka yi sanadin mutuwar fararen hula a karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

Kungiyar ta bayyana cewa amfani da hare-haren sama a matsayin hanyar tabbatar da doka da oda ba ya cikin ka’idojin doka ko na kasa da kasa. Ta ce irin wannan mataki na amfani da karfi fiye da kima ba kawai ya saba wa doka ba ne, har ma yana nuna halin ko-in-kula da sojojin Najeriya ke yi ga rayukan fararen hula da ya kamata su kare.

Amnesty International ta ce hare-haren na ranar Kirsimeti da aka kai wa al’ummomi biyu a Silame sun haifar da mummunar asarar rayuka, inda wasu dangi gaba daya suka rasa rayukansu, yayin da wasu suka kone kurmus a sakamakon wutar da hare-haren suka haddasa.

Kungiyar ta jaddada cewa dokokin jin kai na kasa da kasa sun tanadi cewa a duk lokacin da ake kai hare-hare, wajibi ne a dauki duk matakan da za su rage illar da zai iya shafa rayukan fararen hula.

Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike cikin gaggawa kan yadda aka yanke shawarar kai wadannan hare-haren da kuma yadda aka aiwatar da su, don tabbatar da gaskiya kan musabbabin asarar rayukan fararen hula a jihar Sokoto.