KSITM Ta Fitar da Matsaya Don Inganta Fasaha da Kyautata Ilimi

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, (Katsina Times - 1 ga Disamba, 2024)
  

Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina (KSITM) ta sanar da wasu muhimman matakai da aka tsara domin tabbatar da ingantaccen ilimi da ci gaban fasaha a yankin Arewacin Najeriya. A yayin taron manema labarai da aka gudanar a zauren cibiyar ranar Lahadi 1 ga Disamba, Shugaban Kwamitin Gudanarwa, Injiniya Muttaqa Rabe Darma, ya bayyana sabbin tsare-tsare da nufin mayar da cibiyar ta zama daya daga cikin manyan makarantu a Najeriya cikin shekaru biyu masu zuwa.  

Manyan Matsayoyin da Kwamitin Gudanarwa Ya Cimma 

KSITM ta himmatu wajen shiga cikin harkokin ilimi na duniya ta hanyar shirya taron kasa da kasa kan Amfani da Fasahar (Artificial Intelligent) tare da haɗin gwiwar Jami’ar Al-Qalam da Hukumar ICT ta Jihar Katsina. An tsara wannan taro zai gudana a watan Afrilu, 2025, domin kara karfafa ilimi da ci gaban kimiyya, fasaha, da koyarwa.  

Hukumar Gudanarwar ta amince da kafa sabon kwamitin da za ta taimaka wajen koya wa dalibai kwarewar fasaha ta yau da kullum. Wannan sashen zai ba wa dalibai damar zama masu nagarta da ilimi mai amfani, tare da inganta ayyukan al’umma ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomi na jiha da na tarayya.  

Domin tabbatar da ci gaba mai kyau a shugabanci, an amince da nada Dr. Hindatu Salisu Abubakar, mataimakiyar Rector, a matsayin Rector na rikon kwarya bayan karewar wa’adin Rector mai ci a ranar 12 ga Disamba, 2024. Za a kammala daukar sabbin Rector da Bursar a ranar 20 ga Disamba, 2024.  

Hukumar gudanarwar ta amince da karin girma ga ma’aikata 17 na bangaren ilimi da kuma 16 na bangaren gudanarwa. Wannan mataki yana nuna yadda cibiyar ke martaba ma’aikata da kuma kokarinta na karfafa gwiwar masu aiki.  

An kafa kwamitin da Farfesa Mukhtar El-Kasim ke jagoranta domin gano sabbin hanyoyin samun kudade ta hanyar haɗin gwiwa da wasu hukumomi. Wannan zai taimaka wajen tabbatar da dorewar cibiyar da kara mata karfi a fannin ci gaba.  

An gabatar da shirye-shiryen ci gaban ma’aikata da dalibai domin kara kwarewa da kuma ba su damar koyon sabbin dabaru.  

Hukumar makarantar ta zartar da sabbin dokokin gudanarwa don karfafa shugabanci mai inganci da bin ka’ida, tare da tabbatar da gaskiya da adalci a cikin cibiyar.  

Injiniya Darma ya jaddada kudirin hukumar gudanarwa na tabbatar da KSITM ta zama cibiyar ilimi ta duniya da ke bunkasa ci gaban al’umma. Ya ce, “Za mu hada kai don tabbatar da KSITM ta zama cibiyar ci gaba a Arewacin Najeriya da ma duniya baki daya.”  
 
Sabbin matakan da aka zartar a taron da aka gudanar daga 29 zuwa 30 ga Nuwamba, 2024, sun nuna hangen nesa na cibiyar Fasaha da kirkire-kirkire wajen ci gaban ilimi a fadin jihar Katsina