KAYAYAKIN NADIN SABON SARKIN KATSINA.
- Katsina City News
- 30 Nov, 2024
- 105
A Masarautar Katsina, akwai wasu kayayyaki da ake amfani dasu a ranar da zaa nada sabon Sarkin Katsina, watau ranar da zaa ba Sarki Sandar Girma. Wadannan kayan Gargakiya na Tarihin Masarautar Katsina sun hada da 1. Takobi Gajere, 2. Takobi Bebe 3. Tukunyar Karfe da Kuma 4. Gwauren Tambari.
1. TAKOBI GAREJE( SHORT SWORD). Tarihin wannan Takobi ya nuna itace takobin da Sarkin Katsina Muhammadu Korau ya yanka Sanau. Sarki Sanau shine Sarki na karshe daga cikin Sarakunan Durbi Takusheyi ko kuma Durbawa. Sarki Korau shine Sarki na farko daga cikin zuruar Habe da sukayi mulki a Katsina. Korau asalin zuruarsu Wangarawa ne daga Kasar Mali, sun Fara Zama Yandoton Tsahe cikin Jihar Zamfara ta yanzu. Acikin shekarar 1348 ne Korau yazo Katsina a matsayin Bako, ya tarar da al'adar Sarakunan Katsina ta Kokowa, watau duk shekara ana Kokowa tsakanin Sarki da Wanda ya fito takara. Idan Sarki ya yanka Wanda sukayi Kokowa zai ci gaba da Sarauta, idan Kuma aka yanka Sarki, to sai Wanda ya yanka shi ya Zama Sarki. Korau yayi takara da Sarki Sanau, Kuma yanka shi da Takobi Gajere, wadda itace ake amfani da ita ranar nadin Sabon Sarkin Katsina har zuwa yanzu. Korau ya zama Sarkin Katsina Musulmi na farko. Ita wannan Takobin Gajere itace Sarkin Katsina yake rikewa ga hannun shi a ranar taron Sallah ko Durba.
2. TAKOBI BEBE( THE DEAF ONE).
Itama tana daya daga cikin kayan Gargajiya da Masarautar Katsina take amfani dasu a ranar nada Sabon Sarkin Katsina. Wannan Takobi Bebe Tarihinta ya nuna itace Takobin Sarkin Gobir Yakuba. Katsina sun kwaci wanna Takobin a Fagen Yaki, lokacin da aka kashe Sarkin Gobir Yakuba, aka kwace Takobin aka taho da ita Katsin. Anyi wannan Yaki a lokacin Sarkin Katsina Agwaragi. An gano Takobin a ofishin Sarkin Katsina Magajin Haladu, Sarkin Katsina na karshe daga Habe, lokacin da Masu Jihadi suka Kori Habe daga Katsina cikin shekarar 1807. Takobin ya zama bangare na kayayyakin Sarautar Katsina.
3. TUKUNYAR KARFE.
Tukunyar Karfe tana daya daga cikin kayayyakin da ake amfani dasu wajen nada sabon Sarkin Katsina. Asalinta ta Sarki Korau ce(1348-1398). Korau Yana amfani da Tukunyar Karfe Yana dafama Mayakanshi dauri, domin su Kara kuzari wajen Yaki. Har ma anayi mashi kirari da Korau Mai Tukunyar Karfe. Tukunyar Karfe tana daya daga cikin kayan da ake amfani dasu na Gargajiya wajen nadin Sabon Sarkin Katsina.
4. GWAURON TAMBARI( BACHELOR DRUM).
Gwauron Tambari na Katsina shine babban Tambari daga cikin Tamburan Katsina, Kuma yafi kowane Tambari Tsufa. Ada lokacin ana Yaki, ana amfani dashi don Kiran Mayaka. Misali ana Hawan itaciyar Bawada a rinka kada Gwauron Tambari don a Kira Dakarun Yaki. Ana buga Gwauron Tambari sau goma Sha biyu, idan ana nada Sabon Sarkin Katsina, don girmama shi. Galadiman Katsina ne yake gudanar da wannan aikin. Sannan Kuma Tambura Yana bugashi sau (6) a ranar nada daya daga cikin Hakimman Karaga. Ana Kuma bugashi a ranar nada Sarkin Sullubawa da sauransu.
Wadannan sune kayan Gargajiya da Masarautar Katsina take amfani dasu wajen nadin Sabon Sarkin Katsina.
Alokacin da mulki ya koma ga hannun Turawan Mulkin Mallaka a Katsina a shekarar 1903. Sai Turawan mulkin Mallaka suka bullo da ba Sarki wata Sanda da suka zo da ita daga Kasar Ingila itace ake cema Sandar Girma. Turawan mulkin Mallaka basu amince da su bar Sarki da nadinsa na al'ada ba don kada ya dauka shi keda mulki. Sai suka bullo ba Sarki wannan Sanda don ya dauka cewa akwai fa na gaba dashi watau Rasdan, da D'O da Gwamna. Sarki na farko da Turawa suka Fara ba Sandar Girma shine Sarkin Katsina Abubakar (1887-1905). Har ya zuwa yanzu Gwamna Yana ba Sarki Sandar Girma, a ranar bikin nadin Sabon Sarkin Katsina.
Alh. Musa Gambo Kkfar soro.