Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Fara Biyan Mafi Karancin Albashin Na Naira 70,000.

top-news

Muhammad Aliy Hafiziy, Auwal Isah Musa (Katsina Times)


Biyon bayan tattaunawa na nazari mai zurfi daga Kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa kan mafi karancin albashi na Naira N70,000 wanda ya kumshi wakilan kungiyar kwadago da na gwamnatin jihar Katsina, daga karshe kwamitin ya cimma yarjeniyar sabon mafi karancin albashin.

A daren jiya Juma'a, gamnatin jihar ta Katsina ta sanar da amincewa da sabon mafi karancin albashi na kasa N70,000, a matsayin wanda ita ma za ta aiwatar a matsayin jihar.

Cimma yarjejeniyar na zuwa ne bayan tattaunawar hadin gwiwa da masana daban-daban suka hada da wakilai daga kungiyoyin kwadago,NLC, na kananan hukumomi da da sauransu.

Sabon mafi karancin albashin da gwamnatin ta amince da shi ya hada da gyare-gyaren albashi ga kowane bangare na kafatanin ma'aikatan jihar, wanda dukkan matakai na ma'aikata za su ci gajiyar karin. 

A cewar wakilan gwamnatin jihar, wannan sabon mafi karafin albashi da aka cimma yarjejeniyarsa, ya nuna irin aniyar gwamnatin jihar katsina na ganin an inganta walwala da jin dadin rayuwar ma'aikatan jihar.

Shugabannin Kwadago a ta bangarensu, sun tabbatar da gamsuwarsu game da sabon tsarin albashi, tare da jaddada ci gaba da sadaukarwarsu wajen ganin an inganta rayuwar ma'aikata da mutuncinsu, inda suka bayyana hakan ba kawai zai kawo ci gaba ga ma'aikata kadai ba, har ma share fagen samun hadin kai da ci gaba a jihar ta Katsina.

An bayyana fara biyan sabon mafi karancin Albashin daga wata mai zuwa na Disamban wannan shekara ta 2024.

Cimma matsayar, ta samu sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Katsina, Sakataren gwamnati, da wakilai daga kungiyoyin kwadogo.