An Maka Gwamnatin Nijeriya Kotu Kan Cin Zarafin Talakawa A Abuja
- Katsina City News
- 20 Nov, 2024
- 75
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Wani lauya mai zaman kansa, Abba Hikima, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan wasu manyan jami’an gwamnati da hukumomi, bisa zargin cin zarafin haƙƙin ɗan Adam na wasu ƙungiyoyin talakawa da ke rayuwa a Babban Birnin Tarayya (FCT).
A ƙarar, wanda ke dogaro da Sashe na 34, 35, 41, da 42 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya (wanda aka yi wa gyaran fuska), lauyan ya yi kira da a kare ‘yan Najeriya masu rauni daga cin zarafin da ake zargin wasu jami’ai ke aikatawa. Wadanda ake ƙarar sun haɗa da: Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar Civil Defence (NSCDC), Antoni Janar na Tarayya da kuma Gwamnatin Tarayyar Najeriya .
A ƙarar da aka shigar, Hikima ya bayyana cewa wasu matakai da Ministan FCT ya ɗauka sun kai ga kama mutane ba bisa ƙa’ida ba, tsoratarwa, da karɓar kuɗi daga hannun talakawa. Lauyan ya bayyana cewa wannan lamari ya saɓa wa haƙƙoƙin ɗan Adam kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ƙarar ta ambaci matsalolin da suka haɗa da:
Kama mutane ba tare da gabatar da ƙorafi na doka ba, Karɓar kuɗin cin hanci daga masu neman abinci a kan titi, Tsoratarwa da cin zarafin masu gudanar da ayyukansu na halal.
Lauyan ya nemi kotun ta bayar da umarnin a Bayyana ayyukan da ake zargin jami’an sun aikata a matsayin haramtattu kuma sabawa haƙƙin ɗan Adam ne, Umartar a saki duk mutanen da aka kama bisa umarnin Ministan Abuja ba tare da wata hujja ta doka ba, maidawa waɗanda aka karɓa musu kuɗi ba bisa ƙa’ida ba kuɗaɗensu, Bayar da diyyar Naira miliyan 500 ga waɗanda aka yi wa laifi domin samun saukin cin zarafin da aka yi musu, Tilasta jami’an su bayar da haƙuri ga talakawa da dukkan ‘yan Najeriya, da Samar da dokoki da tsare-tsare da za su kare haƙƙin ɗan Adam, ciki har da wayar da kan jama’a kan haƙƙoƙinsu.
Wannan ƙara ta nuna muhimmancin kare martabar talakawa da sauran masu rauni a cikin al’umma. Hakan zai tabbatar da cewa an kiyaye daidaito tsakanin tsaro da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam a Babban Birnin Tarayya.
Ana sa ran kotun za ta fara sauraron ƙarar nan ba da jimawa ba, lamarin da ka iya shafar tsarin mulki da haƙƙin ɗan Adam a Najeriya.