GWAMNA LAWAL YA ƘADDAMAR DA AIKIN GINA TASHAR MOTA TA ZAMANI A GUSAU, YA SHA ALWASHIN SAMAR DA GURABEN AYYUKAN YI
- Katsina City News
- 20 Nov, 2024
- 55
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na samar da guraben ayyukan yi ga mutanen da rayuwarsu ta dogara ga harkokin tashar mota.
A ranar Litinin ne gwamnan ya ƙaddamar da aikin gina tashar mota ta zamani a kan titin Sakkwato zuwa Zariya a Gusau, babban birnin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, aikin da aka bai wa kamfanin Fieldmark Construction zai haɗa da isassun wuraren ajiye motoci, wuraren hutawa na direbobi, ingantattun na’urorin tsaro, da tsarin bayar da tikitin shiga mota don komai ya zama cikin tsari.
A jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa aikin wani muhimmin bangare ne na ƙudirin gwamnatinsa na inganta ababen more rayuwa a yankunan Gusau.
Ya ƙara da cewa, “Wannan shiri zai inganta tsaro, da inganta samar da kuɗaɗen shiga, da kuma bai wa jiharmu damar yin gogayya da sauran jihohi a faɗin ƙasar nan.
“Wannan katafaren tashar motoci ta zamani za ta ƙunshi kayayyakin zamani da aka tsara domin ɗaukar masu ababen hawa na haya da fasinjoji cikin aminci, inganci da tsari.
“Sauran muhimman abubuwan da ke cikin wannan aikin sun haɗa da wuraren ajiye motoci da za su nufi kowace jiha, ofishin ‘yan sanda, asibiti, tashar kashe gobara, masallaci, ofishin shuganannin tasha, ofishin ƙungiyar ’yan mota, ban ɗakuna, otel ɗin tasha, wurin lodi, kantin sayar da kayayyaki, wurin zubar da shara, rumbun ajiya, garejin gyaran mota da wurin wankin mota.
“A yayin gudanar da aikin, aikin zai ɗauki ƙwararrun ma’aikata da marasa ƙwarewa, kuma da zarar an fara aiki, wurin zai zama cibiyar hada-hadar kasuwanci, wanda zai amfanar da ‘yan kasuwa da masu sauran ayyuka.
Gwamnan ya sake tabbatar da cewa samar da muhimman ababen more rayuwa, kamar hanyoyin da gwamnatinsa ta fara ginawa jim kaɗan bayan hawansa mulki - wasu daga cikinsu an ƙaddamar da su ne a yayin bikin cika shekara ɗaya - yana ɗaya daga cikin mafi inganci hanyoyin bunƙasa harkokin kasuwanci da samar wadata a jihar.
“Bayan tasirinsa na habaka tattalin arziki, wannan shiri wata hanya ce ta ƙawata babban birnin jiharmu ta hanyar hangen nesa mai zurfi na samar da yanayi na zamani kuma mai inganci ga rayuwar jama’armu.
“Da waɗannan kalamai, ina farin cikin ƙaddamar da aikin gina sabuwar tashar mota ta Gusau a hukumance. Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sanya albarka a wannan aiki, ya kuma sa ya zama silar wadata da ci gaba ga al’ummar Jihar Zamfara.”