Alhaji Faruk Jobe Ya Zama Mamba a Cibiyar Nazarin Kwakwaf kan Zamba da Tafiyar da Harkokin Kudi
- Katsina City News
- 14 Nov, 2024
- 133
Suleiman Umar @ Katsina Times
Cibiyar Nazarin Kwakwaf kan Zamba da Tafiyar da Harkokin Kudi ta Najeriya (CIFCFIN) ta ba Mataimakin Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Faruk Lawal Jobe shaidar zama mamba a cibiyar.
Wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban cibiyar, Dr. Isa Salifu, ta ce sun bayar da shaidar ne duba da irin gudunmuwar da Alhaji Faruk Jobe ya bayar a fannin lissafin kudi da kuma binciken zamba.
Wasiƙar ta ce Alhaji Faruk Jobe zai shiga sahun ƙwararru kuma masana da suka sadaukar da kansu don yaƙi da zamba da cin hanci da rashawa da tabbatar da adalci da gaskiya a harkar tafiyar da kudade a mataki gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Wasikar ta ce “cibiyar da ke nazarin da bincike kan zamba da sauran harkokin tafiyar da kudi a Najeriya ita ce kaɗai doka ta san da zaman ta a wannan fannin".
"Dokar kafa ta cibiyar wacce aka kirkiro ta a shekarar 2022, an sanya hannu a kan ta ne a ranar 23 ga watam Disamba, 2022".
Za a gudanar da bikin bayar da shaidar ga Mataimakin Gwamnan ne a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2024, a babban ofishin cibiyar da ke Abuja.