Al’umma Sun Bukaci A Hukunta Soja Da Ɗalibin Da Ya Yi Wa Malamin Makaranta Barazana a Safana
- Katsina City News
- 11 Nov, 2024
- 693
Auwal Isah (Katsina Times)
Al’ummar Sabuwar Unguwa da ke kusa da asibitin Comprehensive Hospital Safana sun bayyana damuwarsu tare da yin kira ga hukumar soji da ta dauki matakin hukunci kan wasu sabbin jami’an soja da suka tada hankalin yankin cikin daren Lahadi. Mutanen yankin sun ce jami’an sun iso tare da wani abokin su sanye da kayan badda kama, inda suka shiga unguwar suka dauki Malamin makarantar sakandare, Junaidu Iliya Safana, tare da jefa al’ummar yankin cikin tsoro.
Wani mazaunin unguwar, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya shaida wa *KatsinaTimes* yadda lamarin ya faru. Ya ce Malamin ya dawo gida bayan sallar Isha’i, ya kwanta, sai wani dalibinsa ya kira shi don jin inda yake, daga nan kuma sai aka kwankwasa kofarsa. Da ya bude, sai kawai jami’an suka dunga bugun shi, suka yi masa duka, suka dauke shi suka fita da shi zuwa wajen gari. Wannan lamari ya sa al’ummar unguwar cikin firgici, suna tunanin 'yan bindiga ne suka kai hari domin daukar Malam Junaidu.
Daukin jami’an tsaron al’umma na C-Watch da 'yan sanda ya sa aka ceto Malamin tare da kama mutane biyu daga cikin wadanda suka kai masa farmaki. Bincike ya tabbatar da cewa ba ‘yan bindiga ba ne; sai dai wasu sabbin jami’an soja ne da suka dawo daga aikin horo tare da dalibin Malam Junaidu.
Rahotanni sun nuna cewa wannan dalibin da ke shirin zana jarabawar karshe, Malamin ya taba yi masa nasiha kan wata mummunar dabi’a, lamarin da bai yi masa dadi ba. Dalibin ya dunga kiransa yana yi masa barazana, yana mai zargin Malamin da bata masa suna.
Dalibin ya zo tare da abokansa sojoji su biyu cikin kayan badda kama, lamarin da ya tsoratar da al’umma sosai da suka dauka ‘yan bindiga ne. Sun cigaba da bugun Malam Junaidu kafin su dauke shi zuwa wajen gari.
Binciken *KatsinaTimes* ya tabbatar da cewa Malam Junaidu yana samun kulawar likitoci a asibiti kuma yana samun sauki. An kama mutum biyu cikin wadanda suka kai masa hari, sai dai dalibin ya tsere zuwa yanzu, kuma hukumomi na ci gaba da bincike.
Al’ummar yankin, wadanda suka bayyana yadda wannan lamari ya tsoratar da su, suna mai la’akari da matsalar tsaro da ta yi kamari a Safana, sun bukaci hukumomin tsaro da ma’aikatar ilimi ta Katsina su dauki matakin da ya dace kan lamarin. Sun yi kira ga hukumar soji da ta binciki wannan jami’ai don tabbatar da an zartar musu hukunci da ya dace, inda suka yi amfani da iko wajen cin mutunci.
"Ina fata hukumomin tsaro da ma’aikatar ilimi za su dauki mataki kan wadannan jami’an da suka kai hari ga daya daga cikin malamanmu jajirtattu. Ya kamata a hukunta su don koyar da darasi ga sauran jami’an tsaro," in ji iyalan Malam Junaidu.