Hukumar CSDA Ta Gudanar da Taron Horaswa Kan Tallafin Ayyukan Jinkai Ga Kananan Hukumomi a Katsina
- Katsina City News
- 08 Nov, 2024
- 130
Daga Sulaiman Ciroma
Hukumar Kula da Ci gaban Al’ummomi ta Katsina (CSDA) ta gudanar da taron horaswa domin bayar da tallafin ayyukan jinkai ga kananan hukumomi a fadin jihar. Wannan taron horaswa ya kasance matakin karshe na shirin hukumar wajen tallafawa al’umma, inda aka koyar da dabaru na kashe kudade yadda ya kamata don samun kayan aiki da gudanar da ayyuka masu inganci.
A yayin taron, hukumar ta gabatar da takardun ceke na kudi ga shugabannin kowace karamar hukuma domin fara aiwatar da ayyuka a yankunansu. Shugaban hukumar, Muhammad Dikko Abdul’aziz, ya jaddada kudirin hukumar na tsayawa tsayin daka wajen ganin ta tallafawa al’umma musamman a wannan lokaci na bukatar ci gaba. Shugaban ya kuma gargadi shugabannin kananan hukumomi da su gudanar da ayyukan bisa gaskiya da rikon amana, yana mai cewa: “Ayyukan da aka dora muku sun hada da kudade, don haka dole ne ku jajirce ku kuma yi aiki da amana domin inganta rayuwar al’umma.”
Shugaban ya kara da cewa, "Mai girma Gwamna ya yarda da wannan hukuma, yana ba mu kudade don tallafawa al’umma ta hanyar ayyukan ci gaba. Dole ne ku dauki wannan aiki da muhimmanci kuma ku gudanar da shi bisa gaskiya, domin wannan aikin hidima ne ga al’umma."
Mukaddashin Manajan Ayyuka, Injiniya Abbas Sulaiman Audi, ya gabatar da kasida a yayin taron, inda ya yi karin bayani kan matakan da ya kamata a bi wajen gudanar da ayyuka don tabbatar da inganci da dorewa.
Daga cikin manyan jami’an hukumar da suka halarci taron horaswar sun hada da Manajan Kudi da Harkokin Mulki, Alhaji Magaji Yusuf Bakori; Mukaddashin Manajan M.E, Ibrahim Dandela; Jami’in Kula da Ilmantarwa da Horaswa, Samaila Balarabe; Malama Rumasa’u, Mataimakiyar Akanta; Malama Habiba Abubakar, Jami’a mai kula da Harkokin Mata; Odita na Hukumar, Malam Ahmed Rabi’u Kankia; da kuma Jami’in Harkokin Saye-Saye, Alhaji Aminu Hassan Gafai.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya wannan hukuma ta gudanar da zaben tantance bukatu wanda ake kira "Participatory Rural Appraisal" a turance, don tantance bukatun kowanne yanki bisa ga abin da al’ummar wurin ke bukata. Wannan tsarin na tantance bukatu ya kasance muhimmin mataki na samar da ayyukan ci gaba da suka dace da bukatun al’ummar yankunan da ake nufin tallafawa.