Hukumar Sufuri ta KTSTA Ta Bude Tashoshin Mota a Kananan Hukumomin Mashi da Ingawa
- Katsina City News
- 07 Nov, 2024
- 181
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, 2024, Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA) ta kaddamar da bude sabbin tashoshin mota guda biyu a kananan hukumomin Mashi da Ingawa, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD,
Da yake jawabi a wajen taron bude tashoshin, Gwamna Radda ya yabawa KTSTA bisa jajircewarta wajen inganta harkar sufuri a fadin jihar. Ya ce gina wadannan tashoshi zai taimaka wajen inganta zirga-zirgar jama'a da samar da sauki ga masu amfani da hanyoyin sufuri a yankunan.
Shugaban KTSTA, Alhaji Haruna Musa Rigoji, a jawabinsa na maraba, ya godewa Gwamnan bisa hadin kai da goyon bayan da yake ba hukumar. Ya bayyana cewa suna sayo sabbin motocin sufuri a duk wata domin kara inganta ayyukan sufuri a jihar.
Hakazalika, Shugaban Karamar Hukumar Mashi, Hon. Salisu Kallah Dankada, ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar bisa ayyukan raya yankin da take yi, yana mai cewa karamar hukumar ta gudanar da dama domin ci gaban al’umma.
Shugaban Kwamitin Sufuri na Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, Hon. Usman Zaharaddeen Sani, tare da sauran ‘yan majalisa ciki har da Hon. Ghali Garba Gidan Mutum Daya, sun halarci taron tare da nuna goyon bayansu ga wannan shirin.
Taron ya samu halartar wasu fitattun jami'an gwamnati, ciki har da shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri, da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati.
Haka kuma, manyan daraktocin hukumar sufuri da sauran jami’an KTSTA, ciki har da sakataren hukumar, Alhaji Ibrahim Kigan, da kwamishinan ma’aikatar ayyuka, sufuri da gidaje, Injiniya Sani Magaji, sun halarci taron.