Gwamnonin Zamfara da Edo Sun Ƙaddamar da Sabon Shirin Inganta Kiwon Lafiya da Musayar Ɗalibai
- Katsina City News
- 01 Nov, 2024
- 31
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yabawa Gwamna Godwin Obaseki bisa ƙoƙarin kawo sauyi da inganta kiwon lafiya a Jihar Edo. Gwamna Lawal, wanda ya halarci bikin ƙaddamarwa da rantsar da sababbin ɗalibai a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Edo (EdoCOHEST), ya bayar da shawarar kafa shirin musayar ɗalibai domin bai wa ɗalibai mata daga Zamfara damar samun horo a Edo.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa bayan ƙaddamarwar, gwamnonin sun zagaya sassan kwalejin don ganin kayayyakin zamani da aka samar. Gwamna Lawal ya jinjina wa Gwamna Obaseki bisa hangen nesansa na samar da kwaleji mai nagarta wanda zai bunƙasa fannin kiwon lafiya tare da haɗa kan al’umma.
Gwamna Obaseki ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Lawal bisa halartar wannan muhimmiyar rana da ta haɗa da ƙaddamar da ginin kwalejin da cika shekaru 60 da kafuwarta.