Gwamnatin Katsina Ta Kaddamar da Kwamitin Gyaran Bangaren Ilimi
- Katsina City News
- 23 Oct, 2024
- 253
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, (Katsina Times)
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta kafa kwamitin musamman da aka dorawa alhakin tantance matsalolin da suke addabar bangaren ilimi tare da samar da mafita ga kalubalen da ake fuskanta. Kwamitin zai mayar da hankali ne kan ilimin firamare, sakandare da na gaba da sakandare, domin gano matsalolin da suke akwai tare da kawo hanyoyin magance su.
A wajen taron kaddamar da kwamitin da ya gudana a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina, Malam Abdullahi Garba Faskari a madadin Gwamnan jihar, ya bayyana muhimmancin aikin kwamitin, inda ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshikin kowanne ci gaban al’umma. "Ilimi shi ne tushen kowacce al’umma mai ma’ana. Duba da yawan kalubalen da ake fuskanta a bangaren ilimi, Mai Girma Gwamna ya kafa wannan kwamitin domin gina wani ginshikin ilimi mai dorewa ga makomar Jihar Katsina," inji shi.
Kwamitin ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban ciki har da Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Mai ba da shawara kan harkokin ilimi, da kuma wakilai daga Ma’aikatun Cigaban Karkara da Harkokin Mata da kuma Ma’aikatar Ilimin Fasaha da Sana’o’i. Sakatare a Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare shi ne sakataren kwamitin.
Daga cikin abubuwan da kwamitin zai duba akwai:
1. Yin cikakken nazari kan halin da ilimin firamare da sakandare suke ciki a Jihar Katsina.
2. Gano matsalolin da ke hana ci gaban tsarin ilimin firamare da sakandare.
3. Kawo hanyoyin magance matsalolin cikin sauki da kuma mai dorewa
4. Ba da shawarwari kan yadda za a inganta ilimin gaba da sakandare a jihar.
5. Samar da wasu shawarwari da za su taimaka wajen bunkasa gaba ɗayan bangaren ilimi.
Abdullahi Faskari ya kuma yi kira ga jama’a da ‘yan asalin jihar masu tunani mai kyau da su kawo gudummawarsu wajen samar da mafita ga kalubalen da ake fuskanta. "Muna kira ga jama’a musamman masu fasaha da tunani mai kyau da su tunkari kwamitin, domin kawo gudummawarsu wajen ganin an samu cigaba," inji shi.
Shugaban kwamitin, Alhaji Falalu Bawale, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Jihar Katsina, ya godewa gwamnan bisa amincewa da kwamitin da aka kafa, tare da bayyana cewa za su yi aiki tukuru domin cika wannan aiki cikin lokaci.
Alhaji Bawale ya bayyana cewa kwamitin zai yi aiki kafada da kafada da dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi domin tabbatar da cewa aikin zai dace da bukatun al’umma. "Zamu dukufa wajen gyaran bangaren ilimi, musamman matakin firamare da sakandare. Wannan nauyin da aka dora mana yana da matukar muhimmanci," inji shi.
Ya kara da cewa kwamitin zai bude kofarsa ga duk wani da ke da shawara mai amfani da za ta taimaka wajen ganin an ceto bangaren ilimi a jihar. "Kofarmu a bude take ga kowa, domin ganin an samu cigaba da inganta ilimi a jihar Katsina," ya jaddada.
Ya kuma yabawa Gwamnan bisa hangen nesansa da jagoranci mai kyau, tare da gode masa kan wannan alhakin da aka dora musu. Alhaji Bawale ya bayyana cewa ya yi imani da cewa tare da hadin kan dukkan mambobin kwamitin, za su kammala aikin cikin lokaci tare da samar da rahoto mai amfani.
"Mun fahimci gaggawar wannan aiki, kuma ina da tabbacin cewa tare da goyon bayan mambobin kwamitin da jama’a, za mu gabatar da rahoto mai inganci da zai taimaka wajen bunkasa ilimi," ya bayyana.
Kaddamar da wannan kwamitin na nuni da muhimmin mataki wajen magance matsalolin da ake fuskanta a bangaren ilimi na Jihar Katsina. Tare da kwarewa da jajircewar mambobin kwamitin, ana fatan kwamitin zai kawo sauye-sauye masu ma’ana da za su inganta ilimin jihar.
A karshe, Sakatare ya sake godewa a madadin Gwamna, tare da addu’ar Allah ya ba da nasara ga wannan aikin. "Muna rokon Allah ya ba mu nasara wajen cimma wannan buri, domin magance matsalolin da ke addabar bangaren ilimi tare da tabbatar da kyakkyawar makoma ga al’umma," inji shi.
Tare da wannan, an kaddamar da aikin kwamitin wanda yanzu zai fara aikinsa na gyaran bangaren ilimi a jihar Katsina.