Zargin Kudin Tallafi a Dan Musa: Ba Gaskiya Bane, Siyasa Ce — Inji Wasu Mutanen Dan Musa
- Katsina City News
- 13 Oct, 2024
- 188
Mu'azu Hassan @ Katsina Times
Wasu mutanen garin Dan Musa sun mayar da martani kan labarin da jaridar Katsina Times ta buga, inda ake zargin cewa kudaden taimakon da gwamnatin jihar Katsina ta bayar ga wadanda ibtila'in 'yan bindiga ya shafa, an yi amfani da su ba bisa ka'ida ba tare da karbar wani kaso daga hannun wadanda aka bai wa taimakon.
Mutanen da suka ziyarci ofishin jaridar Katsina Times sun yi watsi da wannan zargi, suna masu cewa ba gaskiya bane ko kadan, cewa wannan al'amari wata siyasa ce kawai tsakanin wasu manyan 'yan siyasa biyu a karamar hukumar Dan Musa.
Mutanen sun bayyana cewa dan majalisar jihar da ke wakiltar karamar hukumar Dan Musa shi ne ya yi kokarin ganin an samar da wannan tallafi ga mutanen yankin ta hanyar gwamnatin jihar Katsina. Sun kuma tabbatar da cewa ya sa ido sosai don ganin wadanda abin ya shafa sun samu tallafin daidai gwargwado, kuma babu wanda aka tilasta wa ya ba da wani kaso daga cikin abin da aka ba shi.
Jama'ar Dan Musa sun gode wa gwamnatin jihar Katsina da gwamna kan wannan taimako, suna masu rokon a ci gaba da irin wannan taimako a nan gaba. Sun kara jaddada cewa, babu wanda aka nemi ya bayar da wani kaso ko kudi daga abin da aka ba su a cikin garin Dan Musa.
Sun kuma ce, wata kila zargin da ake yi na karbar wani kaso daga taimakon ya shafi wani tallafi ne da aka bayar a garin Maidabino, inda aka samu ce-ce-ku-ce kan yadda aka raba taimakon. Mutanen sun yi kira ga hukumomi da su binciki wannan zargi da aka yi a Maidabino, amma sun jaddada cewa, a garin Dan Musa, ba a karbi ficika ko sisi daga hannun kowa ba.
Mutanen sun kuma yi zargin cewa akwai rikicin siyasa a karamar hukumar Dan Musa, inda wani mai rike da mukami yake neman yi wa dan majalisar jihar sharri da batanci. Sun ce, suna da hujjar cewa wannan mai rike da mukamin yana amfani da wasu yara don rubuta kalaman batanci a kan dan majalisar a shafin Facebook.
Lamarin, a cewar su, ya kai ga hukumomin 'yan sanda sun fara gudanar da bincike, inda suka kama wasu daga cikin yaran da ake zargi don neman bayanai.
Hakazalika, mai bai wa gwamnan jihar Katsina shawara kan matsalar 'yan bindiga ya shaida wa jaridar Katsina Times cewa, aikin raba tallafi na gwamnatin jihar a bude suke yinshi, kuma duk wanda ke da tambaya ko korafi game da aikin su na iya zuwa don samun cikakken bayani.
Kan zargin abin da ya faru a Dan Musa, mai bai wa gwamnan shawara ya ce bai da wata masaniya kan lamarin, kuma har yanzu bai samu korafi a rubuce ba. Sai dai ya tabbatar da cewa, idan har suka samu wani korafi, za su dauki mataki na doka.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.taskarlabarai.com