"Ranar 'Yan Mata Ta Duniya: Karfafa Matasa Don Zama Jagororin Gobe"
- Katsina City News
- 11 Oct, 2024
- 214
Daga Maryam Jamilu Gambo
An Ayyana Ranar 11 ga watan Oktoba a matsayin ranar, Majalisar Dinkin Duniya ce ta bayyana ta don wayar da kan mutane kan kalubalen da 'yan mata ke fuskanta a duniya da kuma inganta hakkokin su
Wannan rana tana mai da hankali kan magance matsaloli irin su ilimi, lafiya, daidaito da kuma kare 'yan mata daga tashin hankali da al'adun da ke cutar da su kamar auren wuri da al'adar yankan al’aura.
Tarihin Ranar 'Yan Mata ta Duniya
Ra’ayin kafa Ranar ya samo asali ne daga "Plan International", wata kungiya da ke fafutukar kare hakkokin 'yan mata.
A shekarar 2011, Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudurin 66/170, inda ta sanya ranar 11 ga Oktoba a matsayin rana ta musamman don jaddada muhimmancin karfafa 'yan mata da tabbatar da ana girmama hakkokinsu a duniya baki daya. An fara gudanar da bikin wannan rana a hukumance a ranar 11 ga Oktoba, 2012.
Kowace shekara, ana tsara rana bisa ga wani batu na musamman da ke magana kan manyan matsalolin da ke shafar 'yan mata. A shekarun da suka gabata, an yi batutuwa irin su “Tare da Ita: Ƙwararrun Ƴan Mata” (2018) da “Muryata, Makomar Mu Daya” (2020). Manufar ita ce jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da 'yan mata ke fuskanta tare da jaddada irin gagarumar gudummawar da za su iya bayarwa ga al'ummarsu da duniya baki daya.
Kalubalen Da 'Yan Mata Ke Fuskanta
'Yan mata suna fuskantar kalubale iri daban-daban a duniya, musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya, da kuma kariya daga tashin hankali da al’adu masu cutarwa. A wurare da dama, ana tauye wa 'yan mata damar samun ilimi mai kyau. Kusan 'yan mata miliyan 129 ba su zuwa makaranta a duniya, inda wasu da dama ake tilasta musu yin auren dole ko aikin yara saboda talauci ko al'adu. Haka kuma, 'yan mata na fuskantar hadarin tashin hankali na jiki da sauransu, sannan galibi su ne ake fatauci da cin zarafi.
A bangaren kiwon lafiya, a kasashe masu tasowa, 'yan mata ba sa samun kulawar kiwon lafiya yadda ya kamata, musamman a bangaren kiwon lafiyar haihuwa. Wannan yana haifar da matsalolin kin cigaba da karatu.
Zuba jari a kan 'yan mata yana da matukar muhimmanci wajen gina duniya mafi kyau. 'Yan mata da aka karfafa su, za su tashi su zama matan da za su bayar da gudummawa sosai ga tattalin arziki, iyalinsu, da al'ummarsu. Samun ilimin 'yan mata musamman yana da matukar tasiri wajen rage talauci da bunkasa ci gaban tattalin arziki. A cewar Babban Bankin Duniya, kowace shekara ta karatu da 'yarinya ta yi za ta iya karawa da kudin shigarta a nan gaba da kashi 20%.
Ta hanyar magance matsaloli irin su auren yara, tashin hankali da ya shafi jinsi, da rashin daidaiton samun ilimi, al'ummar duniya za ta iya samar da duniya mai adalci inda 'yan mata ke da 'yanci su cimma burinsu.
Ranar 'Yan Mata ta Duniya tana tunatar da mu mu ci gaba da fafutukar kare hakkokin 'yan mata, mu gane basirarsu mai ban mamaki, kuma mu goyi bayan ci gaban su wajen zama shugabanni, masu kirkire-kirkire, da masu kawo sauyi.