TARIHIN UNGUWAR MALUMMA, KATSINA
- Katsina City News
- 26 Sep, 2024
- 233
Unguwar Malumma tana daya daga cikin tsafin Unguwannin na Birnin Katsina, domin ta kafu tun lokacin Sarakunan Habe, mulkin Habe a Katsina ya fara daga Sarkin Katsina Muhammadu Korau(1348). Unguwar Malumma tana daga bangaren Unguwannin Haben Birnin Katsina. Daga Kudu tayi iyaka da Gambarawa. Ta ba garen Arewa tayi iyaka da Farin Yaro, ta bangaren Yamma tayi iyaka da Kofar Guga, sannan ta bangaren Gabas ta yi iyaka da Ofishin Gidauniyar Ilimin ta Jihar Katsina.
Malumma Unguwace ta Malamai kamar yadda sunan ta ya nuna. Tun daga farkon mulkin Habe Kasar Katsina ta Kasance babbar cibiyar Kasuwanchi da ilimin ta Kasar Hausa, wannan dalilin yayi sanadiyyar kwararowar Baki Yan Kasuwa da Malamai a Birnin Katsina, Wanda sukayi sanadiyyar kafuwar Unguwannin irin su Sararin Tsako, Tawatunke, Albaba, Malumma da sauransu.
Tarihi ya nuna Malam Usman da Malam Jodoma, Wanda akafi Sani da Wali Jodoma sune wadanda suka kafa Unguwar Malumma ta Birnin Katsina. Su kuwa asalinsu mutanen Borno ne suka yo Kaura suka dawo Katsina. Malam Usman yazo Katsina tareda matar shi wadda aka fi Sani da Maimunatu. Kuma sunzo Katsina tareda Wali Jodoma. A inda Sarkin Katsina ya Basu wurin zama kusa da Gambara, Wanda wurin ya zama Unguwar Malumma. Daga nan suka bude Makarantar Allo suna karantar da mutane ilimin addinin Musulunci. Kamar yadda Hogben SJ da Kirk Greene suka bayyana acikin littafinsu Mai suna ( The Emirate In Northern Nigeria). Lokacin da zaa Gina Masallacin Gobarau an tara Malamai ana neman inda Alqibla take an rasa, Sai Wali Jodoma ya nuna Sandar yace ga inda Qibla take Nan, akayi bincike aka gano hakane, tun daga nan Malaman Katsina suka Rika yi Mashi hasssada, har Tasa ya tashi yabar Katsina, ya koma Kauyen Guga kusa da Kabomo ta Kasar Bakori, Wanda har ya zuwa yanzu Kabarin shi na can a Kauyen. Daga cikin jikokin da Wali Jodoma ya bari a Katsina akwai Marigayi Alhaji Sabiu da Alhaji Ali Babangida da Malam Amiru da Kuma Malam Amiru.
Baya ga harkar Malanta mutanen Unguwar Malumma suna sanaar Noma da sayar da Turare da sauransu. Ance lokacin mulkin Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo (1981-1944) ya nada Marigayi Alhaji Sabiu Maiturae a matsayin Sarkin Turaren Katsina.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.