Katsina Ce Kangaba Wajen Aiwatar da Shirin Tsaftar Ruwa Da Muhalli Na Duniya -SWASH
- Katsina City News
- 20 Sep, 2024
- 235
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Jihar Katsina ta samu yabo a matsayin ta farko wajen aiwatar da shirin "Sustainable Water and Sanitation for All" (SWASH), shirin mai tsawon shekaru shida wanda Bankin Duniya da Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya ke tallafawa.
Babbar tawaga daga Gwamnatin Tarayya, karkashin jagorancin Injiniya Juliet, tare da Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Katsina, Tukur Hassan Tinglin, sun kai ziyara domin duba ci gaban shirin da kuma kammala wasu muhimman ayyuka.
A lokacin tarbar tawagar, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya yabawa kokarin tawagar wajen tabbatar da ci gaban jihar wajen samar da tsaftataccen ruwan sha da ingantacciyar tsaftar muhalli. Faskari ya bayyana cewa, "Jihar Katsina koyaushe tana shirye ta tallafa wa wannan shiri da duk wani yunkuri da zai inganta rayuwar al'umma."
A nata bangaren, Injiniya Juliet ta nuna gamsuwarta da ci gaban da aka samu a jihar, tana mai cewa Katsina ce kadai ta karbi dala miliyan shida a zagaye biyu, wanda hakan ya tabbatar da jagorancinta a wannan shirin. Ta kuma bayyana cewa sauran jihohi har yanzu suna aiki da dala miliyan daya a farkon zango, lamarin da ya sanya Katsina zama abin koyi ga sauran jihohi.
Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, Tukur Hassan Tinglin, ya yi karin haske game da shirin, yana mai cewa, "Jihar Katsina ta kasance a tsakiyar aiwatar da shirin SWASH, inda aka samu nasarori cikin shekaru uku da suka gabata, yayin da saura shekaru uku don kammala shirin."
Tawagar ta kuma kai ziyara don duba wuraren da ake gudanar da ayyuka, don tantance yadda kudade ke gudana da sakamakon ayyukan. Injiniya Juliet ta jaddada cewa muhimmin abu ba kawai samar da kayayyakin aiki ba ne, hadda tabbatar da cewa al'umma, musamman a yankunan karkara, suna amfana da wadannan ayyuka. Ta ce, "Ba kawai batun kwangila ba ne; muhimmin abu shine tabbatar da ayyukan sun isa ga mutane."
Gwamnatin Jihar Katsina tare da abokan huldarta na ci gaba da aiki don tabbatar da dorewar shirin da samun kudade daga irin ci gaban da aka cimma. Babban burin shirin SWASH shi ne karfafa hukumomi domin ci gaba da samar da tsaftataccen ruwa da tsafta har bayan karewar shirin.