KYAUREN GOBIR: YADDA KATSINAWA SUKA KWACE SHI DAGA HANNUN GOBIRAWA.
- Katsina City News
- 14 Sep, 2024
- 269
KATSINAWA sun kwace Kyauren Gobir daga hannun GOBIRAWA a lokacin mulkin Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo( 1771-1789) Tarihi ya nuna Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo ya kawo ma KATSINAWA hari na Yaki, a lokacin mulkin shi, inda ya biyo ta shiyyar Maradi, kafin ya shigo Katsina. Anyi wannan Yaki a Garin Dankaishi dake cikin Nigeria ta yanzu. KATSINAWA sukayi nasara a wajen Yakin.
Ance KATSINAWA sunyi sahu kamar guda bakawai(7) a wajen Yakin, Kuma kowane Sahu akwai Kwamandan Yaki. Dan Galadima na Abu Dan Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo shine Kwamandan Yaki a GOBIRAWA a wannan Yaki, ance ya fasa sahu a daya da sahu na biyu na KATSINAWA, ga Sahu na 3 Wanda Uban Dawakin Katsina yake shugabanta aka kashe Dan Galadima na Abu Dan Bawa Jan Gwarzo. Ganin haka Sai Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo yace a mazaya a mazaya akai iri gida. Katsina karkashin Sarkin Katsina Agwaragi suka rakasu har bakin Kofar Birnin Naya ta Kasar Gobir, suka cire Kyauren Gobir suka taho dashi Katsina Wanda har ya zuwa yanzu Kyauren na GOBIRAWA yana Nan Birnin Katsina.
Ance bayan kwana (40) da wannan Yaki ciwon zuciya ya kama Bawa Jan Gwarzo ya rasu( Dr. Yusuf Bala Usman Ya rubuta haka acikin littafinshi Mai suna "The Transformation of Katsina").
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.