KIWON LAFIYA; CUTAR SHAN INNA
- Katsina City News
- 31 Aug, 2024
- 217
Cutar shan inna (Polio) cuta ce da ke kama wani ɓangare na ƙwaƙwalwar ɗan Adam, wadda ke haifar da mutuwar wani sashe na jiki. Kwayoyin cuta ne ke kawo wannan ciwo, waɗanda ba su da magani, sai dai a yi maganin abin da marar lafiya yake nuna wa (watau kwayar cutar virus). Ana iya ɗaukar cutar ta hanyoyi kamar haka:
1. Ta hanyar iska.
2. Ta shan gurbataccen ruwa.
3. Yin amfani da kayan aiki da mai wannan cuta ya yi amfani da su, ko kuma aka yi masa amfani da su.
Wannan cuta tana zama cikin jikin ɗan Adam har tsawon kwanaki bakwai zuwa goma sha huɗu (7-14), kafin wanda ya kamu da cutar ya fara nuna alamomin ita wannan cuta ta shan-inna. Har ila yau, akwai wasu abubuwa da ke jawo cutar, kamar haka:
1. Rauni (ciwon da ya fasa fatar jiki).
2. Ta hanyar allura a duwawu ko hannu.
3. Matsanancin motsa jiki.
ALAMOMIN CUTAR SHAN-INNA
Alamomin cutar shan inna sun kasu kashi biyu kamar haka:
Kashi na Farko: Alamomin farko na shigar cutar. Za a ga waɗannan alamomi kamar haka:
1. Cutar na farawa ne kwatsam.
2. Matsanancin zazzaɓi.
3. Ciwon kai.
4. Kasala.
5. Mura tare da zubar majina daga hanci.
6. Jijiya za su kama ciwo, musamman baya da na kafa.
7. Wuya zai zama ba zai iya juyawa ba.
8. Rashin yin fitsari.
Waɗannan alamomi ana iya ganinsu daga rana ta farko ta kamuwa da cutar zuwa sati ɗaya (1-7). Da zarar an ga ɗaya ko fiye da ɗaya daga cikin waɗannan alamomi, sai a hanzarta zuwa asibiti domin neman magani. Allah Ya sa mu dace; amin.
YADDA ZA A GANE WANNAN CUTAR
Alama ta biyu ita ce ta mutuwar wasu sassan jiki. Hakan na faruwa ne sakamakon illar wannan cuta mai haddasa shan-inna da ta yi a cikin ƙwaƙwalwa. Waɗannan alamomi ana iya gane su ta hanyoyi kamar haka:
1. Ta hanyar auna bayan-gari domin a gane cutar.
2. Ta hanyar auna ruwan laka.
3. Ta hanyar auna majina.
Irin waɗannan aune-aune a asibiti ne kawai ake yinsu.
RIGA-KAFIN KAMUWA DA CUTAR SHAN INNA
Hanyoyin riga-kafin cutar shan inna sun haɗa da:
1. Ta hanyar yin allurar riga-kafi tare da diga wa jarirai da ƙananan yara ruwan foliyo.
2. Da zarar an haifi jariri, sai a yi masa allurar riga-kafi tare da diga ruwan foliyo, sannan a ci gaba da kai shi asibiti kan ka’ida kamar yadda malaman lafiya suka ummurta domin amsar sauran alluran, tare da ruwan foliyo. Yin hakan yana da matuƙar mahimmanci saboda yana hana aukuwar wannan cuta.
3. Ta hanyar tafasa kayan aiki a asibiti. Ita ma wannan hanya tana taimakawa ƙwarai da gaske.
4. A guji matsanancin motsa jiki. Idan za a motsa jiki, ya kasance kadan-kadan.
5. Idan an ji ciwo, a yi ƙoƙarin neman magani domin hana aukuwar irin wannan cuta ta shan inna.
Da fatan za a kula sosai domin tana daga cikin cututtukan nan shida waɗanda ke hallaka ɗan Adam.
Daga Littafin Kula da Lafiya Na Safiyya Ya'u Yamel