NNPCL SUN TAIMAKAWA MASU LALURAR CUTAR IDO A LEGAS ....sama da mutane dubu daya suka amfana
- Katsina City News
- 29 Aug, 2024
- 235
Daga 0lufemi O Soneye
Fassarar Hassan M Tukur
@ Katsina Times
A kokarin da take yi na inganta rayuwar al'amomin da ke kusa da kamfanin NNPCL, Mutane dubu daya ne zasu amfana da Shirin kula da lafiyar ido na ikko (Lagos).
A sakon da ya aike wajen kaddamar da Shirin kula da lafiyar ido, shugaban bunkasa jari na kamfanin, Mr Bala Wunti ya ce wannan shiri wani bangare ne na Hukumar da Mallam Mele Kyari yake jagoranta ke yi na inganta rayuwar al'amomi a kasar nan.
Mr Bala Wunti Wanda ya samu wakilcin Mrs Bunmi Lawson ya tuno cewa Shirin kula da ido na matakin farko ya yi tasiri ga mutane 1,853 da suka samu kulawa to idanunsu a kyauta.
Ya bayyanar da cewa Shirin da aka gudanar a ikko ( Lagos) a shekarar 2022 ya duba Mutane 2000 Kuma daga ciki likitoci sun duba Mutane 1,199 wadanda suka samu tabarau na inganta ganinsu, a yayin da Mutane 1,310 sun samu Magunguna kala-kala da Kuma wasu Mutane 189 daga bisani.
Mr Bala Wunti ya Kara bayanin cewa Shirin kula da idanun na NNPC na da nufin hana qalubalen rashin gani da ka iya zama ka baya ga al'umma ta hanyar yin tiyatar ido bada tabarau da sauran Magunguna na hana makanta.
Ya bada tabbacin cewa masu halartar neman lafiyar ido zasu cigaba da samun kulawa da basu shawarwari kan abinchi mai gina jiki da samun hutu na musamman.
Olufemi Soneye
Chief Communications officer
NNPC Ltd
Abuja
28/08/2024