Tatsuniya Ta 45: Labarin Janniya
- Katsina City News
- 22 Aug, 2024
- 317
Akwai wata mata mai suna Janniya. Suna zaune ita da kishiyarta tare da mijinsu cikin lumana. Wannan mata kuma tana da garken shanu. Daya daga cikin shanun kuma yakan yi magana kamar mutum.
Wata rana, uwar Janniya tana zaune da kishiyarta suna hira, sai ta ce da kishiyar: "Ina jin fa na kusa mutuwa. Idan na mutu, ki kula da Janniya."
Da kishiyar ta ji haka sai ta ce: "Haba! Ai ko ba ki fada ba, zan kula da shi, ai dana ne."
Sai uwar Janniya ta ce: "To, na gode da kika yi wannan alwashi."
Bayan kamar kwana hudu da yin wannan zance, sai uwar Janniya ta rasu.
Kishiyar ta mallaki shanun da uwar Janniya ta bari. Suna nan suna zaune, kullum sai kishiyar ta zuba wa Janniya magunguna na asiri iri-iri a cikin abincinsa. Amma duk sanda Janniya ya zo cin abincin, bijimin nan na shanunsa yakan hana shi ci, sai ya rinka rera waka yana cewa:
"Janniya Jannati,
Ba uwa ba ce,
Kishiyar uwa.
Janniya Jannati,
In za ta ba ka tuwo,
Tuwo da magani,
Ka tona rami,
A gindin turkena,
Ka binne tuwon,
Kar ka ci, Janniya."
Kullum haka yake faruwa, amma duk da rashin cin abinci kamar yadda ya kamata, wannan bai sa Janniya ya rame ba. Yau da gobe sai kishiyar uwar ta gane wannan bijimi ne ke tona mata asiri, sai ta matsa wa mijinta ya amince a yanka bijimin.
Shi kuma bijimin duk ya ji abin da aka shirya, sai ya ce da Janniya: "Idan an yanka ni, ka ce a ba ka kai da kafafuwana da kayan ciki. Sai ka binne su. Yin haka zai karya duk wani makiru da za ta yi maka."
Da aka yanka bijimin, sai Janniya ya roki a ba shi duk wadannan abubuwan. Aka ba shi, shi kuma ya je ya binne. Sai kishiyar uwar ta ci gaba da ba shi sammu iri-iri, amma saboda ya yi abin da bijimin ya fada, duk makircin da take yi bai kama shi ba. Kullum Janniya sai kara kyau yake, ita kuma bakin ciki na damunta.
Kamar yadda wani magana ya ce, "bakin ciki kan kashe irin wadannan mutane." Haka kuwa aka yi. Kishiyar uwar ta ci gaba da lalacewa, har ta mutu daga karshe.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa:
1. Duk wanda ya yi kokarin canza hukuncin Allah, karshensa nadama da halaka.
2. Mugun nufi ba ya kashe dan kurciya.
An ciro wannan labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman.