Matsalar Tsaro a Katsina: 'Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane da Dama Kuma Sun Yi Garkuwa da Mutane Hudu a Unguwar Nasarawa
- Katsina City News
- 17 Aug, 2024
- 259
A daren jiya, unguwar Nasarawa dake cikin garin Kurfi, karamar hukumar Kurfi, ta sake fuskantar wani harin 'yan bindiga. Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun shiga yankin ba tare da wata fargaba ba, inda suka yi awon gaba da mutane hudu daga cikin al'ummar unguwar. Wannan danyen aikin ya jefa mazauna yankin cikin tsananin tashin hankali da fargaba.
A cikin wadanda aka sace, akwai wata mata mai jarirai sabuwar haihuwa da wasu ƙananan yara. Wannan abin takaici ya kara jefa al'ummar Nasarawa cikin damuwa, kasancewar har yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan halin da wadanda aka sace suke ciki.
Bayan sace mutane hudu, 'yan bindigar sun yi wa mutane da dama raunuka, kuma har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka jikkata ba. Maharan sun yi amfani da muggan makamai a yayin wannan harin, wanda ya yi sanadiyyar jikkata wasu da dama. Wannan hari ya nuna matsalar tsaro ke kara samun cikas a jihar Katsina, musamman ma a yankunan karkara.
Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan wannan lamari, wanda ya sake dagula lissafin tsaro a yankin. Al'ummar yankin na cigaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa don tabbatar da tsaron rayukan su da dukiyoyinsu.
Yawaitar irin wadannan hare-hare a jihar Katsina na nuna yadda 'yan bindiga ke cigaba da cin karensu babu babbaka, lamarin da ke kara sanyaya gwiwar jama'a game da kokarin da ake cewa ana yi na kawo karshen wannan matsala.