Gwamna Dauda Lawal Ya Bayyana Muhimmancin Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Zamfara
- Katsina City News
- 16 Aug, 2024
- 258
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) da ke Gusau a matsayin muhimmin ginshiƙin samar da ƙwararrun malamai a makarantun gwamnati na jihar.
A ranar Laraba, Majalisar Gudanarwar Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta kai wa Gwamna Lawal ziyarar ban-girma a gidan gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ziyarar ta kasance ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da kwalejin.
Gwamna Lawal ya nuna matuƙar jin daɗinsa da ziyarar, tare da jaddada muhimmancin bai wa kwalejin dukkan goyon bayan da ta dace. Ya bayyana cewa al'ummar Zamfara sun daɗe suna cin gajiyar kwalejin, inda ya ce, “Yan uwana mata kusan biyar sun yi karatu a FCET.”
Ya ƙara da cewa, “A cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin da ta gabata ta kasa biyan kuɗin jarrabawar NECO da WAEC ga ɗalibanmu. Duk da haka, mun biya bashin, wanda yanzu ya zama tarihi. A baya-bayan nan, ɗalibanmu sun samu nasara a jarrabawar NECO ta ɗalibai masu hazaƙa, inda Jihar Zamfara ta zama ta farko a Arewacin Najeriya kuma ta biyu a ƙasar baki ɗaya.”
Gwamna Lawal ya kuma bayyana cewa suna gudanar da gyare-gyare a makarantu sama da 290 a faɗin jihar, tare da samar da kayan karatu na zamani da horar da malamai, inda ya jaddada cewa FCET za ta taka rawar gani a wannan yunƙuri.
Shugaban Majalisar Gudanarwar Kwalejin, Farfesa Muhammad Bashir Nuhu, ya yaba wa gwamnan bisa ba da fifiko ga fannin ilimi. Ya ce, "Kwalejin FCET ta zama abin alfahari ga jihar, kuma muna godiya da matakan da kuke ɗauka don inganta ilimi a Zamfara."