Ranar Matasa Ta Duniya: Hadin Gwiwa Kungiyoyi Da Gwamnati sun shirya Taro A Katsina
- Katsina City News
- 15 Aug, 2024
- 218
A ranar Alhamis, 15 ga Agusta 2024, Hadakar Kungiyoyin Matasa tare da Ma'aikatar Matasa da Wasanni ta jihar Katsina sun gudanar da taron Ranar Matasa ta Duniya. Taron ya gudana ne a dakin taro na Hukumar Kananan Hukumomi ta Jihar Katsina, inda ya samu halartar dimbin matasa daga dukkan kananan hukumomin jihar.
Kungiyoyin da suka shirya taron sun hada da Kungiyar Hadin Gwiwar Matasa ta Kasa da Kasa (International Youth Mercy Corps Community), Cibiyar Matasa ta Kasa reshen jihar Katsina, tare da hadin gwiwar Ma'aikatar Matasa da Wasanni ta jihar Katsina (Katsina State Ministry of Youth and Sports Development).
Taken taron na wannan shekara shi ne: "Zaman Lafiya Shine Ginshikin Arziki Da Ci Gaban Al'umma; Mu Rungumi Zaman Lafiya". An gudanar da lakcoci a taron da harsunan Turanci da Hausa, tare da haska kalubalen da ke fuskantar matasa a yau da kuma hanyoyin da za su dora rayuwarsu bisa turbar da ta dace domin samun ingantacciyar makoma.
Daga cikin wadanda suka gabatar da lakcoci a taron sun hada da kwararru daga bangarori daban-daban kamar likitoci, farfesoshi, jami'an gwamnati, hukumomin tsaro da wakilan kungiyoyin matasa.
Wasu daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi sun hada da Dr. Bala Abdullahi Husain daga Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua Katsina, Dr. Mukhtar Alkasim na Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, da Daraktan Hukumar Ci Gaban Matasa da Wasanni ta jiha, Alhaji Sani Yahaya.
Sauran wadanda suka yi jawabi sun hada da Wakilin Kwamishinan 'Yan Sanda na Jiha, DSP Daniel Eneche, Shugabar Kungiyar Zaburantar da Matasa Mata "We Girls," A'isha Aliyu Marafa, da Wakilin Kwamandan Rundunar Civil Defence ta Jiha.
Lakcocin sun mayar da hankali kan batutuwa kamar: Waye Matashi? Hanyoyin Da Matashi Zai Tsayu Da Kansa, Abubuwan Da Za Su Bunkasa Matashi A Rayuwa, da Gudummuwar Matashi Wajen Bunkasa Tattalin Arzikinsa.
Bugu da kari, an gudanar da tattaunawa kan rayuwar yau da kullum da kalubalen da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya, tare da ba da shawarar yadda matasa za su amfana da shirye-shiryen da gwamnati ta tanadar musu domin su dogara da kansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 12 ga watan Agusta a matsayin Ranar Matasa ta Duniya, domin duba matsalolin matasa da kuma hanyoyin warware su a duk fadin duniya.