‘DA NIJERIYA MUTUM CE DA KABILUN AFIRKA SUN BAUTA MA TA’
- Katsina City News
- 28 Jul, 2024
- 432
HAJIYA ABUN NA-BARNO KATSINA
A ranar Juma’a, 24/5/2024, Malam Aliyu Ibrahim Kankara ya ziyarci Hajiya Abun Na-Barno, wata fitattar ‘yar siyasa, kuma wadda ta yi yawo a tsakanin wasu kasashen Afirka domin yada manufofin NPC. Hajiya Abu, ta yi waiwaye a kan asalinta, rayuwarta da gwagwarmayar ta. Ga yadda hirar ta su ta kasance.
Kankara; Hajiya, mu na son mu ji sunanki da inda aka haife ki. Yaya kuruciya ta kasance a zamaninku?
Hajiya Abu: Sunana Hajiya Zainabu, Abu. An haifeni a cikin unguwar ‘Yantaba da ke nan cikin birnin Katsina. Sunan mahaifina Malam Nuraddini, amma an fi kiransa da lakanin Ladan. Sunan kakana Malam Abdul’Aziz, Shi, ya yi zama da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944) Sarki Dikko ya nada shi ya zama sarkin fulanin Kasar Mani. Daga baya sai mahaifinmu, Malam Ladan ya yi ma Sarkin Taushin Katsina, Waziri. Da ni da Ibrahim Nahabu mai kukuma da Na-Barno, uwarmu daya, ubanmu daya. Nice karamar su.
Yanda abin ya ke shi ne, shi da kan sa Sarkin Katsina ya nemi ya nada mahaifinmu Sarkin Taushi domin sun gaji kidan taushi din. To, a daidai wannan lokacin kuma sai ga Sarkin Taushi ya zo daga wani gari, Goran Namaye ta Kasar Sokoto a da, ya na yi ma Sarkin Katsina wakar taushi. Sarki Dikko ya ce ma sa mi ka ke so? Ya ce shi Katsina ya ke so ya mayar da shi. Mahaifinmu na tare da shi. To, za’a ba shi Malam Ladan sarautar sai ya ki, ya ce ba ya so, amma a bai wa Sarkin Taushi, watau Mamman Dan Sodangi.
Sarkin Taushi. Da ka ji ana cewa ‘Dan Sodangi’ to ai Abdul’Aziz shi ne Sodangi din. Ya dauki so ya dora ma sarkin taushi tunda ya na tare da mahaifinmu. Domin, a gidanmu ya zauna lokacin da ya zo ya na bako. Kai, kusan, saboda ma kakana sarkin taushi ya zauna kasarnan ta Katsina.
Kankara: Ashe ke nan, shi Malam Abdul’Aziz, fitaccen mutum ne a cikin Katsina?
Hajiya Abu: Da mahaifin Alhaji Ahmadu Na-Funtuwa, Sa’In Katsina, Malam Abdulkadir da iyayenmu, tushensu daya don, dan mace da dan namiji su ke. Saboda haka, mu ‘yan uwa ne na kusa da kusa ma. Dukanmu a unguwar ‘Yantaba mu ka tashi. Ga gidanmu ga gidansu. ‘Ba ka ji ba ana ce ma sa ‘ko cikin birni, unguwarsu ‘Yantaba?’ Ai a ‘Yantaba su ka tashi. Ko da ka ji ana cewa Abba siri-siri (33) watau kanen Sa’I, ai tare mu ka yi was an kasa da shi. A lokacin ma da ya zo ta’aziyyar kanwarsu, Hajiya Aina’u da ta rasu, ai a dakin tsohuwata ya zauna ya sha hura, su ka yi zumunci, su ka yi hira. Bayan ya bar dakin tsohuwarmu da kwana arba’in da daya (41) ya rasu. Ka san, shi Sa’I, kamar taba ya ke, shiga cikin rayi ya ke. Duk wanda ya yi hulda da shi dole sai ya ji ya na son shi, ya na kaunarsa. Kada fa ka manta, mahaifinsa, Malam Abdulkadir ya yi mataimakin Alkali na Funtuwa, kuma ya yi bukadi na Sarkin Maska Sambo, sannan ya komo Katsina.
Kankara: Hajiya, ina asalin wannan unguwa da ake kira ‘Yantaba?
Hajiya Abu: Taba gari ake dakawa a unguwar, ana sayarwa. A lokacin, sai, duk jama’ar unguwar su na yin sana’ar, in banda ‘yan kalilan, irin iyayenmu. To, daga baya sai ma aka rinka tace duddugar ana kai ma masu laifi, watau daurarru ko ‘yan bursuna, a gidan Yari su na kullawa su na sha. To, wannan shi ake kira ‘angale’ kuma.
Kankara: Akwai wani abu da za ki iya saurin tunawa a lokacin yarintarki?
Hajiya Abu: Malam Aliyu, da wayau na mu ke bin Sarki Muhammadu Dikko cikin kasuwannin Katsina, ya na yi wa ma’auna da ‘yan kasuwa wa’azi, ya na rokonsu su daina tauye mudu, su yi adalci wajen cinikayyarsu. A wannan shekarar ne aka yi yunwa da ake kira ‘Yar Balanga. Na san Kankara tun lokacin Sarkin Pauwa Mudi, zafi ba’a bi ta gabanka, mijin indo ‘yar Barhaza, gugar karfe sha kwaramniya’.
Aliyu, na san Dantura. Da wayauna lokacin da ya yi zamani. Dantura ya fara zama Yari na farko a cikin birnin Katsina. Da ya rasu, sai dansa, Dodon kanti, mahaifin Hajiya Murja ya ce ba za ya riki mukamin Yari ba, sai ya tafi ya bude kanti ya rinka ciniki da kwarori.
Kankara: Ke nan, kin a nufin, shi ne kakan Alhaji Dahiru Bara’u Mangal na wajen uwa?
Hajiya Abu: Ko shakka babu.
Kankara: Zancen karatun boko fa, an yi ?
Hajiya Abu: Hmmmm, Malam Aliyu Kankara ke nan. Mu mu ka fara bude makarantar boko ta gidan Malam Barmo. A lokacin duk fadin Katsina babu aji ko guda. Da mu ka shekara guda sai aka rufe makarantar Malam Barmo, bayan an gina makarantar da ke Rafindadi, watau Central Primary School, sai mu ka koma can. Ajinmu daya da Abba 33 kanen Sain Katsina. A nan, sai mu ka shekara uku. Aka yi jarabawa mu ka ci. Da zan wuce makarantar Midil in karasa a Rafukka sai iyayena su ka hana, su ka dakatar da ni. Daga aji hudu na fita daga makaranta, kafin in tafi Kamaru. Hajiya Hassu Iro Inko, kawata ce, ajinmu daya.
Kankara: To, an ci gajiyar karatun bokon?
Hajiya Abu E, babu shakka. Na taba yin aikin gwamnati mana. Na yi aiki a gidan rediyon Katsina. Na karanta littattafai kamar su Tarihin Annabi SAW juzu’I na uku da sauran littattafai na addini. Wasu kuma littattafan da ba su shafi addinin ba da na karanta ba zan iya tuna su ba farat da garaje.
Kankara: Kafin ki tafi Kamaru ke nan?
Hajiya Abu: Kwarai, kafin in tafi Kamaru.
Kankara: Ko a iya tuna wasu mutane da aka yi hidima ko amintaka da su a baya?
Hajiya Abu: Ina gaisawa da Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman, tun ya na dan doka, kafin ya zama Magajin garin Katsina. Na san Sufeto Sa’idu Barda, mun yi hidimar arziki tun ya na dan doka shi ma. Na san Sufeto Yusufu Shema dan doka. Na san Hajiya Amina Kulkula diyar jakiri, ‘mai mutanen banza’ mun yi gwagwarmayar NPC tare da ita.. Da aka nada Ibrahim Kumasi Sardaunan Katsina, ina tsaye,. Sarki Kabir ya waigo, na ce ma sa ‘ranka ya dade’. Ya ce ma Kumasi ‘ga jakadiya na ba ka’. Kumasi ya ce ‘ta fi karfina’. Sarki ya ce ‘na ba ka hakanan’.
Kankara: Mu je ga zancen siyasa, Hajiya. An yi siyasa?
Hajiya Abu: Mu, NPC mu ka yi, mai zafin ma kuwa. Su Gambo Sawaba, su su ka yi NEPU, ita da su Yusuf Maitama Sule, Danmasanin Kano. Mun yi kamfe da Musa ‘Yar’aduwa da Dauda Mani da Abu Duwan da sauransu. Malam Aliyu, mun sha wahalar siyasa. Mun yi gwagwarmaya ta kafa NPC. A kamfe, mun kwana takwas (8) a Kurami ba tare da mun wuce Funtuwa ba. Da an gama magana sai a fara wata sai a fara kulla wani abin kuma. Sai a fasa wucewa. Wanshekare kuma, sai an shirya wucewa, sai kuma a kulla wani abin, daga nan kuma sai zancen tafiya ya shiririce.
A wurin kamfe, na sha sukar Aminu Kano da manufofinsa. Shi ma haka, a kamfe, ya sha sukar mu da manufofinmu. Bari in ba ka wani dan takaitaccen labari. Watarana, saboda gasa da takara ta siyasa, sai Malam Aminu Kano ya aika na je wajensa a Kano. Sai ya na yi ma ni zancen cewa: Haba Hajiya, in shiga ‘Yantaba da Unguwar Alkali ta Katsina, in auri ‘yar uwarki, sannan ki rinka zagi na a wajen kamfe. Mi ya kawo dalilin haka?
Sai na ce ma sa ‘ka dai je Unguwar Alkali ka auri A’isha ‘yar can, amma ba ka shiga ‘Yantaba ba. Mu ka yi ta gardama. Mu ka yi sama da shi, mu ka rikito kasa. Na ce ma sa ‘ga ka nan dan kadan babu afki’, yanzu ko canye ka na yi sai in yi ta shan ruwa don na san matanka ba za su neme ka ba. Danmasanin Kano ya ce ma sa ‘na fada ma ka idan ka kira ta sai ka gaji da dariya don za ka sha surutu’. Shi ma kan shi, Aminu Kano din ya yi ta dariya.
Sannan, zamana a Kongo da Gabon duka, siyasa ce na yi ma su irin manufofin NPC. Shi ya sanya na yi amintaka da Umar Bango wanda ya yi shugaban Kasar Gabon. Mun yi siyasa guda tare da shi, tare mu ka sha gwagwarmaya. Ko a shekarun baya ma da ya rasu saida na koma har can Gabon din na yi ma su gaisuwa. Ka ga, ai yanzu dansa ke yin mulkin ko?
Kankara: Hajiya, a kwatanta siyasar da da ta yanzu.
Hajiya Abu: Na san Gambo Sawaba. Kawata ce, tare mu ka yi gwagwarmayar siyasa. Su, sun yi NEPU. Gambo haifaffar Guru ce. Amma, sabili da cin amana na siyasa da ‘yan siyasar, ka duba irin wahalar da ta sha a rayuwa akan NEPU, da daurin da ta sha, ba
ta bar komi ba a rayuwarta, domin hakanan ta rasu, babu gidan kirki babu mota. Na san Asabe Reza, ita ma hakanan ta rasu ba ta da komi. Jagoran tafiyar NEPU, shi ma hakanan ya bar Duniya bai ajiye komi ba. Mu, mu ka yi siyasa ta akida, ta amana. Amma, yanzu siyasar neman kudi ake yi.
Siyasar yau ta sanya ‘yan siyasa sun koma makwadaita, mayaudara, ba su da amana, sai karya.
Yanzu ba siyasa ake yi ba sai sata da munafunci da karya. Sai digirgiren banza, alhali tsawo bai kai ba. ‘Yan siyasa sun koma matsorata, sun koma ‘yan koren kasashen turawa. Don, ana amfani da su ana kashe Afirka da tattalin arzikinta. A yau, ‘yan siyasa sun zama ‘yan amshin Shatan Amerika da Faransa da sauran kawayen su. Amerika ta firgita Duniya ta hana mutanen Afirka zama lafiya. An hana mu noma. An koro mu daga kauyukanmu, daga gonakinmu, kiri-kiri, mu na ji mu na gani, noma ta gagare mu, zama gidajenmu ya gagare mu. To, duk sherin Amerika ne. Duk kasar Afirka da ta ke da arziki, Amerika da Faransa ba za su taba bari su zauna lafiya ba. Su kuma ‘yan siyasarmu, munafukai ne, ba su tarar komi sai son sata da kwadayin mulki, shi ya sanya su key i ma Amerika abin da ta ke so. An mayar da mu bayi, kaskantattu. An firgita mu, an hana mu zauna mu fuskanci rayuwa mai kyau. Amerika da Faransa sun kawo ma na Boko Haram da sauran ta’addanci, kuma sai, su ka yi nasarar zabar rubabbu, ‘yan uwanmu, watau fulani, marasa ilimi, jahilai, marasa imani. To duk wadannan abubuwa, Amerika ba ta samu nasarar gabatar ma na da sub a sai da ta samu yarjewar ‘yan siyasar mu. Idan ba su yard aba to za su sa kafar wando daya da Amurka. Su kuma, saboda kwadayin mulki, dole su ka amince, su ka yarda ake tafiya akan hakan.
Saboda arzikinmu da kimarmu da tsarinmu na rayuwa da yawan ma’adinai, Amurka ba za ta bari mu zauna lafiya ba. Ta kunno kai ta hada mu fada da fulanin daji jahilai. Wannan shi ne maganar gaskiya. An jarraba raba mu da daidaita mu a lokuta daban-daban, ta hanyar yaki da rarraba kawunanmu ta hanyar amfani da addini, amma Allah Bai yarda ba. Sai yanzu su ka samu galaba ta hanyar amfani da fulanin daji, marasa tunani, ma su tunanin dabbobi.
Ka duba ka ga Paul Biya, shugaban Kamaru. Kusan, ya shafe shekara ta kai arba’in da biyu (42) ya na mulki. Ya zarce shekaru casa’in (90) a Duniya. Duk daurin gindin Amerika ne. Yanzu, har ta kai, da kun yi magana yanzu, zuwa anjima ya manta. Yanzu, dan shekara 90 wane tunanin yi ma Kasarsa aiki mai kyau za yay i? Wai shi ne shugaban kasa kamar ta Kamaru?
Mulkin Buhari asara ne, don, bai kawo ma na komi ba sai ci-baya a kasarmu da sauran kasashen Afirka da ke dogaro da mu wajen bunkasa arzikin su. Duk bala’in da mu ka shiga ciki na rashin tsaro da abin da ya haifar da lalacewar naira, da rugujewar arzikinmu, duk mulkin Buhari ne sala, shi ne dalili. Buhari ba ya jin magana kuma ba ya daukar shawara. Ba ya da mashawarta na kirki, kuma, duk barayi ya tara, sun kewaye shi, wadanda, su, ba ci-gaban Nijeriya ke gabansu ba sai neman wawashe baitulmali.
Kankara: Bari mu ji, a wannan gaba, tarihin zuwanki Kamaru da sauran kasashen makwabta.
Hajiya Abu: Na zauna Afirka ta tsakiya da Kongo Kinshasha da Kongo Birazabil da Gabon. Na yi siyasa. A Siraliyon aka nada Sa’In Katsina, Ahmadu Na-Funtuwa, sarkin Hausawa na can. Zuwana Kamaru ukku (3).Sauran zuwa guda biyu duk da kai na na je.
Zuwana na farko ya haddasa ne ta hanyar zuwa neman yayana, Ibrahim Nahabu mai kukuma da ya tafi Kamaru ya tare ba tare da izinin iyayenmu ba. Ba mu kuma san inda ma ya nufa ba, a’a, shi dai ya tafi yawon Duniya. Ana nan ana nan, uwarmu, kullum rayinta bace, ta na tunani. Abin ya dame ta. Ba mu san inda ya nufa ba, sannan babu wani labarin sa. Toh, rannan, sai, marigayi, Alhaji Garba Bakori, wanda ya yi Dallatun Katsina ya hadu da wani mutum a Kaduna, shi kuma mutumin, ya zo daga Duwala ta Kasar Kamaru akan wani aiki na su na gwamnati. Su na cikin hira sai Garba Bakori ya ce ma sa, shi mutumin Katsina ne. Sai mutumin y ace, ai kuwa a can Duwala, sun a tar da wani mutumin Katsina, ana ce da shi Ibrahim Nahabu mai kukuma, ya na yin waka. Har ma, daga can Duwala, ya kan haura ya tafi Afirka ta tsakiya da Gabon don wasa, amma dai, babban ubangidansa a can, shi ne Ahmadu Ahijo, shugaban Kamaru.
Sai Garba Bakori , ya ce, ai dama ana ta nemansa, an yi tsammanin ya rasu, ba ya da rai. Ya ce ma sa, idan ya komo Katsina za ya je har gida ya shaida ma tsohuwarsa cewa ya samu wanda ya san inda Ibrahim Nahabu yak e, kuma ya na nan zanue, lafiya lau, da ran sa. Ya kuma shirya da mutumin nan cewa idan ya je ya shaida ma sa cewa ya zo gida, ana son ganin sa, cewa mahaifiyarsa na nemansa. Mutumin ya yi alkawarin insha Allahu za ya shaida ma sa. Ya kuma rubuta takarda y aba mutumin don ya kai ma Nahabu din.
Da Garba Bakori ya zo Katsina sai ya tafi hard akin mahaifiyarmu ya shaida ma ta, ta kuma yi murna kwarai da gaske. Ya kuma shaida ma ta cewa ya ma ba da takarda a kai ma sa.
Toh, ana nan akan hakan sai na kasa daurewa, na kagara in gad an uwana, don in share ma mahaifiyarmu hawaye. Rannan, sai na shirya n ace ma ta zan tafi Kaduna. Daga Kaduna, ba tare da ta sani ba sai na wuce Kamaru, na bi ta Yola. Alhali ban san can wajen ba don, ban taba zuwa ba. Ni dai, kawai na kama hanya.
Malam Ali, ka san hanyoyin can wajen bas u da kyau, ko a yanzu ma ballantana a wancan lokacin. An yi ma ni aiki a asibiti na afendis, kafin in tafi. Wallahi ban ida warkewa ban a kama hanya don in gano inda dan uwana ya ke. To, mun sauka wani gari, Maiganga a cikin Kasar Kamaru, wajen wasu kabilu da ake kira Baya, watau, su, Bayawa ne, saboda rashin kyawon hanya, sai aikin da aka yi ma ni ya bude. Nan na kwanta asibiti.
Kankara; Subhanalillahi. Innalillahi wa inna ilayhirraji’una. A wane yanki ne, ko jiha?
Hajiya Abu: A yankin karamar hukumar Tinyar, wajen wani yanki da ake kira Tibati. Toh, sai, daga cikin fasinjojin da mu ka tafi da su kuma, sai aka ba wani daga cikinsu sako, idan ya isa Duwala ya shaida ma Ibrahim Nahabu cewa, ya yi bakuwa, wata kanwarsa, ta taho wajen sa amma lalurar rashin lafiya ya same ta a hanya, ta na kwance a asibiti a wannan garin. Da ya isa, ya same shi, ya shaida ma sa. Cikin dare sai ga Nahabu ya iso, shi da abokansa, a firgice, su ka tarar da ni kwance, an sake yi ma ni dunki, an yi ma ni allurai, amma ina barci. Ko da na ji muryarsa sai na falka, na bude ido. Ina ganin sa sai ya ce ma ni ‘kwanta ki huta, ki yi barci, sai kin tashi mu gaisa’
Toh, a takaice, Malam Aliyu, wannan tafiya ta farko ta farauto yayana ita ta bude ma ni ido na gane kasashen nan guda uku, da ke kusa da juna.
Na farauto shi ya taho gida, don, ce ma sa na yi idan ya na son kada mahaifiyarmu ta mutu saboda tunanin sa to ya tafi gida ta gan shi. Jin haka, shi ma sai hankalinsa ya tashi, ya ji shi gidan kawai ya ke son ya taho. Amma, na riga shi dawowa. Shi, sai da ya kimtsa, ya kara kwanaki tukun. Amma, bayan ya dawo gida, ya sake komawa, har ma yay i aure can ya kuma haifi ‘ya’ya. Yanzu ma, mai bi ma babban dansa na can Kamaru tunda shi dan kasa ne. Shi ke yin wakokin kukuma irin na mahaifinsa.
Kankara: Hajiya, kin yi yawo a tsakanin kasashen Afirka, yaya za ki kwatanta halayyar mutanen Afirka din da ta mutanen Nijeriya a wancan lokacin?
Hajiya Abu Malam Aliyu, Nijeriya babbar kasa ce, mai tarin albarka da kasar noma da arziki marar misali. Hatta kasashen Turai,, daga wajenmu su ke cin bashi, ka tambaya ka ji. Saboda baiwa da ilhama ta jama’ar Nijeriya kusan duk kasashen Afirka da Duniya baki daya ana ganin mutuncinmu da darajarmu.
Duk Afirka, babu kasa mai yawan lunguna da garuruwa kamar Nijeriya. Malam Ali, wallahi na shiga garuruwa a Afirka da idan ka yi rantsuwa, a matsayinka na haifaffen Nijeriya za’a yarda da kai, duk abin da ka ce za’a aminta da shi. Wallahi, saboda mun fi kowacce kasa a Afirka yawan jama’a. Mu ne ma su addini mai tsari, ma su rayuwa mai tsari, ma su gaskiya, ma su amana. Duk inda dan Nijeriya ya ke ana girmama shi, ana mutunta shi, a wancan lokacin.
Aliyu, duk Afirka babu kasa da ta kai Nijeriya tsari na karatun boko da ma yawan ‘yan bokon. Duk Afirka babu kasa mai tsari na sarauta da kuma yi ma sarautar biyayya kamar mu. Mun fi sauran al’ummar Afirka ilimi na addinin musulunci da ilimin zamantakewa da jama’a da neman zaman lafiya da kowa. Mu na da tsari da rayuwa mai kyau, mai inganci. Ko dai kai ba musulmi ba ne, to ka na da tsari na irin n aka addinin. Ba mu da kazamta, ba mu da wauta, mu ba shashashai ba ne. Duk inda mu ka je a Afirka da sauran sassan Duniya ana girmama mu, an aba mu girman da ya dace, ana mutunta mu. Ba n ace ma ka, lokacin da Sa’I, Ahmadu Na-Funtuwa ya je Siraliyon, shi su ka nada Sarkin Hausawan can ba? Sannan, ya yi ma Kwame Nkurumah kamfe a lokacin da yay i takarar shugaban kasar Ghana. Duk mi ya jawo haka? Sabili da girman mu da mutuncinmu da hazakarmu da wayewarmu a tsakanin al’ummar Afirka. Da dan Aibari Kwas ko dan Guinea ko dan Ghana ko Kamaru ya gad an Nijeriya sai ya ga kamar ya ga wani halitta daban wanda ya ma fi mutum daraja. Saboda mi na ce ma ka haka? Don, a lokacin duhun kai, kafin su samu ‘yanci, yawanci, kasashen, ba su da wayewa, ba su da ilimi, ba su da tsari na zamantakewa da mutane, ba su da arziki, Galiban za ka tarar wasu al’ummomin zaune su ne a kusa da ruwa ko koramu, wasu na zaune a bisa duwatsu, wasu ma ba su da sutura. Kai wasu ma kusan tsirara su ke yawo, ga shi babu addinan kirki. Rayuwar dai, gata nan, abu babu kyau, babu inganci. Turawan mulkin mallaka da su ka shige su daga baya su ka mulke su, su, su ka koya ma su iya sa sutura, su ka nuna ma su yanda ma tsarin rayuwa yak e, sannan su ka sanya su hanyar sanin addinai.
Mu ko, a Nijeriya, dama, tun kafin zuwan Turawa, mu na da tsarin sarauta da zamantakrwa da iya zama da mutane da addini mai kyau. Wannan ya sanya, a wadancan lokuta, duk kasar Afirka da dan Nijeria ya je, sai ka ga mutanen kamar ma su bauta ma sa saboda sun ga wanda ya fi su. Kai, in gajarce ma ka labari, da Allah Ya sanya Nijeriya mutum ce, wallahi da kabilun Afirka da dama sun bauta ma ta saboda girmamawa.
Ga dai kasashen Afirka da arzikin amma ba su san yadda za su yi su tattala shi ba. Ba su san hanyar da za su bi mu gino shi su sarrafa shi ba. Saboda babu wayewa, babu ilimin kirki.
Bari in ba ka wani dan takaitaccen tarihi. Ko ka san cewa ma fi yawancin mutanen Afirka ba su da kaciya? Saboda rashin wayewa da rashin ilimi, yawancin maza a kasashen Afirka ba’a yi ma su shayi ko kaciya. Ba su ma santa ba, wallahi. Sai ka ga mutum ya shekara tamanin (80) amma ba ya da kaciya. Mu ko nan, da yaro ya shekara bakwai (7) za’a kai shi a yi ma sa shayi. Haka ka’idar ta ke, sabili da bin tsarin addinanmu guda biyu. An yi wani bako a nan Nijeriya wai shi Mista Kurmo daga Afirka ta Kudu. Nan ya ga ana yi ma yara kaciya. Ya ce, minene wannan? Sai aka ce ma sa ‘kaciya ce da ake yi ma kowanne namiji’. Ya tambaya, shin ko minene muhimmancin kaciyar? Aka shaida ma sa. Sai ya ga ai su a can Afirka ta Kudu ba’a yi ma maza wannan abin. Shi ya sanya ma kowa ke yin rayuwa hakanan. Nan take sai ya amince shi ma ya na son a yi ma sa kaciya. Aka shaida ma Sarki da kuma sauran hukumomi. Su ka amince. aka kai shi asibiti aka yi ma sa shayin. Ya kwanta nan asibiti, ya yi jinya, gwamnati ta dauki nauyin abin. Da ya warke ya sanya wandonsa ya koma gida. Can ma din, sai su ka yi ta al\ajabi, ga Mista Kurmo ya zo Nijeriya ya samu lafiya.
Kankara: Mu je ga batun Alhaji Mamman Shata Katsina. Mun san ya yi ma ki waka. Ko minene sala?
Hajiya Abu: Na san Shata tun ina matashiyata a nan cikin birnin Katsina, idan ya zo wajen su Bature jikan Dada da Bature Kanada da wazirin ayyuka, Abu Jika. Amma, ba mu san juna ba sosai sai tsakanin 1956 a lokacin da ya ke zuwa otek din Sufeto Yusufu Shema, dandoka. Abin da ya faru shi ne, ni, ina da gida, sai ban sa kowa ciki ba, na ba wani yaro ya na kwana ciki. Rannan, sai Sa’in Katsina, Alhaji Ahmadu Na-Funtuwa, dan uwana ya rinka kai Shata gidan ya na kwana, watau ganin cewa kamar kayana kamar kayansa ne tunda dan uwana ne, kuma gas hi ya ga a cikin gidan, akwai dakuna da babu kowa a cikin su.
Rannan, sai Shata yay i kyautar gidan ga wani mutum, ga zaton cewa kamar Sa’I ya bar ma sa gidan.
Kankara: Shi Shata, ya san cewa gidanki ne?
Hajiya Abu: Wannan, Allah Ya bar ma kanSa sani. Duk abin da na fada na yi karya. Shi ke nan, sai na dauki takardun gida na tafi kotu wajen Alkali. Aka kira Shata, aka maida Magana. Da aka sake zama sai aka fahimci cewa wanda Shata y aba gida, shi ma ya sayar da shi. Sai na tayar da rigima cewa ban yard aba dole sai Shata ya biya ni gida na.
To, ana cikin neman ma ni wani gidan, kafin a saya ma ni, sai ya yi ma ni wannan waka, ya na cewa: Abun Na-Barno ta ki zancen nan/Karuwa ba ta haihuwar Garba, kuma, karuwa ba’a ba ta da Garba ta rika.
Ya yi ma ni wakar ne a matsayin maida ma ni da martini cewa na yi ma sa wulakanci, tunda, shi maroki ne, ya na ganin kamar ya kamata in bar ma sa gidan kyauta ba sai ma na yi karar sa ba.
Kankara: To, Hajiya, mi ya sanya ya kara, ko raba ki a cikin wakar Dan Lagai Lagai?
Hajiya Abu: Ai majingina ya samu. Yanzu, ka na nasa kwai ba tare da ka na da zakara a cikin aljihu ba? Ai, ka dubi kalmar da ya fadi. Ai sai ya jefo Garba Dan Lagai Lagai cikin batun sannan jifar da ya yi ma ni na zancen za ya sauka daidai a bias kai na. Shi ko Garba Lagai Lagai, ai ka gad an uwana ne. Iyayenmu da kakanninmu daya. Ni, kamar uwa ce a gare shi a bangaren dangantakarmu. Tunda kuma ya ga mu na gaisawa da Garba, to nan ya samu mashiga.
Kankara: Ban da wannan zancen, ya yi ma ki wata waka ta daban?
Hajiya Abu: E, ya yi ma ni wasu wakokin guda biyu daga baya, amma duk ba su yi nisa ba, bayan ya saya ma ni gidan ke nan kuma mun shirya.
Kankara: Daga karshe, a cikin hidimar siyasar da ku ka yi ta NPC, mi ki ke saurin tunawa, farat da garaje?
Hajiya Abu: Wanda na ke saurin tunawa da shi, shi ne jagoran ci-gaban Arewa, mai kishin Kasa, Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto. Duk irin salon mulkin kasashen Afirka da ka gani, to irin salon mulkin Sardauna Ahmadu Bello ne. Duk tsarinsa ne kasashen Afirka su ka rinka bi har su ka kai ga ci-gaba, suma Wannan ya sanya ake girmama mu, ana ganin kimarmu, mu, Nijeriya a matsayin Kasa. Sannan, abu na biyu da na ke saurin tunawa shi ne, da NEPU da NPC duk manufofi daya ke gare su, amma hakanan mu ka yi ta rigima, mu na kashe junanmu.
Kankara: Hajiya, mu na godiya kwarai da gaske. Allah Ya saka da alheri. Na bar ki lafiya.
Hajiya Abu: Nima ina godiya, Malam Aliyu.
Aliyu Ibrahim Kankara, ya rubuto daga Katsina,
Alhamis, 18/7/2024