BAYANI AKAN SARAUTAR BANGAJE, A MASARAUTAR KATSINA.
- Katsina City News
- 21 Jul, 2024
- 357
Daga cikin Buwarorin Sarkin Katsina akwai wata Sarauta Maisuna "BANBAJE", wadda baa badata Sai amintaccen Sarki.
Babban aikin Bangaje, shine Yana shiga gaban Zagage ranar Taron Sallah ko Durba, ko Kuma Sallar Jumaa' a lokacin Sarki na zuwa Jumaa bisa doki.
2. Hakanan Kuma idan Majasirdi ya shirya dokin da Sarki zai hau, ya daura Sirdi da Linzami, to Bangaje zai zo ya banki dokin, ya tabbatar da ya dautu daram.
3. Hakanan Kuma, akwai wata Takobi da ake zuwa da ita Sallar JUMA'A, to aikin Bangaje ne daukar Takobin. Ita wannan Takobin tana da Tarihi sosai, ko yanzu da baa hawan doki zuwa JUMA'A zaa ganta cikin Motar Sarki Zagi ya riketa saboda tsaron Sarki, domin Sarautar Zagi tana daya daga cikin Sarautun Tsaro a Kasar Hausa, harda Katsina. Al'adar wannan Takobin ita Koda yaushe tana cikin Kube, idan aka zarota daga Kube to sai ta yanki wani ko Tasha jinin wani, a lokacin ana Shariar Musulunci ansha zartas haddi da ita.
Bangajen da zamu iya tunawa sune wadanda sukayi Sarautar Bangaje daga lokacin mulkin Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo zuwa yanzu kamar haka:--
1. Bangaje Muntari
2. Bangaje Na'taala
3. BANBAJE Abubakar Danboyi
4. Bangaje Kabir Abubakar Danboyi.
Musa Gambo Kofar soro.
21-07-2024.