Engineer Hassan Sani Jikan Malan Ya Yi Kira Ga Shugaba Tinubu da Yan Majalisar Zartawa Kan Matsin Rayuwa

top-news

Wani dan kishin kasa, Engineer Hassan Sani Jikan Malan, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da yan majalisar zartawa na tarayya da sauran masu rike da mukamai na alfarma, da su dauki matakin gaggawa na rage matsin rayuwa da mutanen Najeriya ke ciki.

Engineer Hassan ya bayyana bukatar daukan matakin gaggawa kan wannan lamari a matsayin su na masu fada a ji, lokacin da ya zanta da manema labaru a Katsina. Ya ce matsin rayuwa na ci gaba da ta'azzara a kowace rana a fadin kasar nan.

Ya bayar da misalin rashin tsayayyen farashin kayan masarufi, man fetur, da gas a gidajen mai da sauran kayayyaki, wanda ya ce yana kara wahalar da yan Najeriya.

Engineer Hassan Sani Jikan Malan ya kuma kara yin kira ga yan majalisan dattawa da na wakilai da su kawo wa wadanda suka kada musu kuri'u gami da masu karamin karfi dauki ta samar masu da abinci da tallafin jari na sana'o'i domin rage radadin da suke ciki.

Matashin dan siyasa ya nuna gamsuwa bisa hukuncin da kotun koli ta yanke dangane da ba kananan hukumomi 774 tare da babban birnin tarayya damar cin gashin kansu, yana mai cewa hakan ci gaba ne a damokaradiyya kasancewar su ke kusa da al'umma.

Engineer Hassan Sani Jikan Malan ya bukaci yan Najeriya da su jajirce wajen yin addua na samun damuna mai albarka a wannan shekara tare da neman dauki wajen Allah na magance matsalar tsaro da ke damun wasu yankunan kasar nan.

NNPC Advert