Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ɗaukar matakan da suka dace domin samar da zaman lafiya da tsaro a matsayin ginshiƙan cigaban ƙasa nan masu ɗorewa.
Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai Malam Rabiu Ibrahim, ya faɗa a sanarwa ga manema labarai cewa Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin jawabin sa na farko a matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Gidauniyar Cigaban Jihar Neja (NSDF), wadda wata ƙungiya ce ba ta siyasa ba da ke bayar da shawarwari don kawo cigaban jihar.
Idris ya ce babu yadda za a yi a samu cigaba idan babu zaman lafiya da tsaro, ya ƙara da cewa abu ne wanda Shugaba Tinubu ya fahimta sosai, kuma gwamnatin sa tana baƙin ƙoƙari matuƙa a wannan fage a wani ɓangare na gagarumin tsarin da take bi don sauya fasalin ƙasar nan.
Ya ce: “Zan yi amfani da wannan damar in jaddada alaƙar da ke tsakanin cigaba, zaman lafiya, tsaro da kuma ababen more rayuwa. Waɗannan abubuwa suna da alaƙa da juna, kuma suna ƙarfafa juna. Ba za a iya samun cigaba mai ma’ana ba idan babu zaman lafiya da tsaro, haka kuma amfanin cigaba kan kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan wata haƙiƙa ce da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya fahimta sosai, wanda ya sa gwamnatin sa ke zuba jari sosai a waɗannan fannonin a matsayin wata dabarar da za ta sauya fasalin ƙasa gaba ɗaya.”
"Mai girma Shugaban ya bayyana ƙarara cewa babu zaɓi a batun tsaro; shi ne ginshiƙin da ke ɗauke da duk sauran abubuwa na cigaban ƙasa. Hakan ne ya sa, a ƙarƙashin jagorancin sa, Gwamnatin Tarayya ta dage, ba kama hannun yaro, wajen ƙarfafa hukumomin tsaron mu. Manufar haka a bayyane take: a samar da yanayin da ya dace inda al'umma za su haɓaka, harkokin kasuwanci su inganta, kuma cigaba ya kafu sosai."
Ministan ya yaba wa tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Zubairu Dada, wanda shi ne shugaban farko na NSDF, bisa jajircewar sa da hangen nesa, tare da alƙawarin zai gina kan nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin sa.
Ya ce: “A yau, a gaban mai girma Gwamna, ina sake jaddada cikakken goyon bayana ga manufar wannan ƙungiya: wato amfani da ƙwarewa da basirar da 'yan Jihar Neja suka mallaka don bunƙasa cigaban jihar mu abar so.”
Ministan ya jaddada cewa kasancewar ƙungiyar ba ta da nasaba da siyasa na taimakawa wajen haɗa kai da aiwatar da ayyukan cigaba.
Ya ƙara da cewa, “Mu ƙungiya ce da ba ta da nasaba da siyasa, kuma wannan ne ƙarfin mu. Bambancin ƙwarewar da muke da shi yana ba mu damar zama wata gada da mai saka mana shauƙi: a haɗa jihar da Gwamnatin Tarayya, a haɗa gwamnati da masu zaman kan su, a haɗa mafarki da aiki.”
A yayin ƙaddamar da sababbin membobin Hukumar gudanarwar NSDF ɗin, Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya yaba da hangen nesa na waɗanda suka assasa hukumar, tare da tabbatar da aniyar gwamnatin sa ta hanzarta aiwatar da manyan ayyukan cigaba a faɗin jihar.
Ya yi la'akari da cewa duk da a jikin Neja aka ɗebi kashi 75 na Gundumar Babban Birnin Tarayya (FC), amma mafi yawan yankunan Jihar Neja da ke maƙwaɓtaka da FCT gidajen baragurbi ne.
Bago ya ce: "Mun nuna bajinta a cikin 'yan watannin da suka gabata wajen ƙwace dukkan filayen da ke kewaye da Dutsen Zuma domin gina sabon birni, kuma kafin ranar 29 ga Mayu, 2025, za a fara ginin sabon ƙaramin Gidan Gwamnati a bayan Dutsen Zuma.”
Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙulla haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin raya hekta 50,000 na ƙasa a yankunan Suleja da Tafa zuwa wani birni na zamani da zai yi gogayya da wasu daga cikin manyan unguwannin birnin Abuja.
Gwamnan ya yi alƙawarin ci gaba da aiki tare da 'yan hukumar NSDF a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin sa na gaggauta cigaban Jihar Neja.
Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Noma da Wadatar Abinci, zai shugabanci hukumar tare da Minista Idris, wadda ta ƙunshi manyan fitattun ‘yan asalin Jihar Neja.