Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kasance cikin gwamnonin da aka zaɓa domin raka Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu zuwa taron Shugabannin Ƙasashe 20 (G20 ) da za a gudanar a Afirka ta Kudu.
Taron, wanda za a yi ranar 22 da 23 ga Nuwamba, zai tattaro shugabannin ƙasashe mambobi na G20 gaba ɗaya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa dukkan ƙasashen da ke cikin G20 za su halarci wannan babban taro.
Haka kuma, ƙasashe goma sha shida za su shiga matsayin baƙi, tare da wasu ƙasashe shida da ke wakiltar ƙungiyoyin tattalin arziki na yankuna daga Afirka, Caribbean da Gabashin Asiya.
Sanarwar ta ce, “An zaɓi Gwamna Dauda Lawal a matsayin ɗaya daga cikin tawagar Shugaba Bola Ahmad Tinubu da za su halarci taron G20 a Johannesburg, Afirka ta Kudu.
Sauran gwamnonin da za su kasance a tawagar sun haɗa da na Osun, Filato, Gombe, Katsina, Neja, Enugu da Nasarawa.”
Taron shugabanni na G20 na wannan shekarar shi ne matakin ƙarshe da ke tattara dukkan aikace-aikacen da aka gudanar tsawon shekara ta hannun tarukan ministoci, ƙungiyoyin aiki da ƙungiyoyin haɗin gwiwa.
Haka kuma, an bayyana cewa a cikin kwana biyu da taron zai gudana za a yi zaman taro uku, inda za a tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da kasuwanci, kuɗaɗe, ƙalubalen bashin duniya, sauyin yanayi, tsaron abinci, adalci, ma’adanai masu muhimmanci, ingantaccen aikin yi, da rawar da fasahar AI za ta taka a ci gaban duniya.
Sulaiman Bala Idris
Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara
18 ga Nuwamba, 2025