Tasirin Yajin Aiki a Katsina: Makarantu da Bankuna sunbi sahu
- Katsina City News
- 05 Sep, 2023
- 824
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A wani Zagayen gani da Ido da Wakilin Jaridar Katsina Times yayi a wasu Ma'aikatu, sunga yanda aka garkame su babu wani alamu na Aiki, hakan ya nuna cewa yajin aikin na kungiyar Kwadago NLC yana tasiri.
Makarantun Firamare da Sakandare zuwa manyan makarantu na gwamnati duk sun rufe, haka Bankuna, da wasu ɓangarori na Gwamnati, saidai abinda muka lura dashi yajin aikin bai taɓa wasu cibiyoyin lafiya ba, inda wakilin mu yaga anata shige da fice a Asibitin jihar da wasu kananan asibitoci.
Mun iske wata da tazo duba lafiyarta Asibitin kofar kaura, ta shedamana cewa idan ba yanzu da mukai magana ba bata ma san ana yajin aiki ba. Tace yanzu zata shiga Asibiti ganin likita.
A ra'ayin jama'a: da yawa daga cikin wadanda mukaji ta bakinsu basa goyon bayan yajin aikin.
Wasu da suke makwaftaka da bankuna sun cemana da safiyar ranar Talata Bankunan sun bude daga bisani kuma suka rufe.
Kungiyar ta NLC dai ta bayyana cewa zata shiga yajin aikin gargadi na kwana biyu domin kin amincewa da janye Tallafin man fetur da kuma kin amincewa da tallafi da gwamnatin tace ta bayar ga jihohi domin rage Raɗaɗin halin rayuwa.
Shin ko yayaya yanayin yajin aikin yake da tasiri a yankunan ku?