Daga Yanzu Kananan hukumomi zasu dunga Cin gashin Kansu -Kotun Koli
- Katsina City News
- 11 Jul, 2024
- 424
Kotun koli ta yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnonin jihohi 36 na tarayya kan cin gashin kan kananan hukumomi.
A cikin karar, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya nemi cikakken ‘yancin cin gashin kai da kuma raba kudade kai tsaye ga kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Ya bukaci kotun kolin da ta yi amfani da sashe na 1, 4, 5, 7 da 14 na kundin tsarin mulkin kasar domin bayyana cewa gwamnoni da majalisun jihohi suna da hakkin tabbatar da tsarin dimokuradiyya a mataki na uku.
A hukuncin da ta yanke wanda mai shari’a Emmanuel Agim ya karanta, kotun kolin ta bayyana cewa ba bisa ka’ida ba ne gwamnoni su rike kudaden da aka tanada na kananan hukumomi (LG).
Mai shari’a Agim ya ce kin amincewar da gwamnatin jihar ta yi na cin gashin kan kananan hukumomi ya shafe sama da shekaru ashirin.
A cewarsa, tun daga lokacin ne kananan hukumomi suka daina karbar kudaden da aka tanadar musu daga gwamnonin jihohin da ke aiki a madadinsu.
Yayin da yake lura da cewa ya kamata kananan hukumomi 774 na kasar nan su sarrafa kudaden su da kansu, ya yi watsi da matakin farko na wadanda ake kara (gwamnonin jihohi).
Mai shari’a Agim ya ce AGF na da ‘yancin kafa wannan kara da kuma kare kundin tsarin mulki.
Don haka, kotun kolin ta bayar da umarnin a biya su kudaden kananan hukumomi daga asusun tarayya kai tsaye daga yanzu.