Ba Matsala Ce Ta Haifar Da Neman Ba'asi a Masarautar Katsina ba - Gwamnatin Jihar Katsina
- Katsina City News
- 30 Jun, 2024
- 502
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ba wata gagarumar matsala ce ta haifar da bukatar jin ba'asi a masarautar Katsina. Kwamishinan yaɗa labarai da al'adun gargajiya na jihar, Dakta Bala Salisu Zango, ya tabbatar wa BBC cewa ana neman ba'asi ne kan gazawar wasu hakimai wajen halartar hawan sallah, duk da shirin da aka yi tun farko.
Dakta Zango ya bayyana cewa, "Wannan tunanin mutane ne, kuma ba za ka hana mutane faɗin abin da ke bakunansu ba." Ya ƙara da cewa masarautun gargajiya suna ƙarƙashin ikon gwamnatocin jihohi a duk fadin Najeriya, kuma gwamna na da ikon yin duk abin da ya ga dama kan masarautun.
"Babu inda gwamnatin Katsina ta ce za ta fasa wata masarauta a jihar, amma wannan ba yana nufin gwamnati ba ta da ikon yin hakan ba," in ji kwamishinan. "Iko ne na gwamna ya yi yadda yake so bisa daidai a jiharsa, muddin zai yi wa al'ummar jiharsa daɗi."
Kwamishinan ya jaddada cewa masarautun gargajiya a ƙarƙashin ikon gwamna suke a kowace jiha, kuma gwamna na da ikon yin duk abin da ya ga ya dace domin al'ummar jiharsa.
Rikici tsakanin sarakuna da gwamnoni na neman zama ruwan dare musamman a yankunan arewacin Najeriya. Ko a baya-bayan nan, an ga yadda ake samun sabani a Kano kan batun masarautun jihar, bayan da gwamna Abba Kabir ya sauke wasu sarakuna tare da naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kano, bayan gyaran dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta yi.
Haka zalika, a makon da ya gabata, gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya aike da ƙudurin gyaran dokar masarautu gaban majalisar dokokin jihar domin yi mata gyaran fuska, wani abu da wasu ke ganin tamkar rage wa Sarki Musulmi ƙarfin iko ne.
Masu sharhi dai suna ganin cewa galibi abin da ke janyo saɓani tsakanin sarakunan gargajiya da gwamnonin jihohi shi ne zargin rashin nuna goyon baya ga jam'iyyun gwamnonin a lokacin yaƙin neman zaɓe. Sai dai kwamishinan yaɗa labarai ya ce a jihar Katsina ba wannan matsalar ce, domin a cewarsa sarakunan Daura da na Katsina ba su tsunduma kansu cikin harkokin siyasar jihar ba.
"Sarakunan jiharmu biyu na Daura da na Katsina sun ja girmansu, sun kare mutuncinsu ba su shiga harkokin siyasa ba," in ji shi.