Gina Titin Jirgin Ƙasa Kilomita 700: Tunubu Yahau Kura Babu Takunkumi, inji Atiku

top-news

Tinubu Ya Hau Kura Ba Takunkumi, Zai Kashe Adadin Kasafin Kuɗaɗen Jihohi 36 Da Abuja, Wajen Gina Titin Jirgin Kasa Na Kilomita 700’, Cewar Atiku Abubakar 

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa salon ɗirka gadangarƙamar satar maƙudan kuɗaɗe ne kawai da har Ministan Sufuri, Dave Umahi ya bayyana cewa titin jirgin ƙasa da ake ginawa daga Legas zuwa Kalaba, zai lashe Naira tiriliyan 15.6.

Atiku wanda ya yi takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023, ya ce Naira tiriliyan 15.6 fa ba ƙaramin kuɗi ba ne, domin sun kai adadin kasafin kuɗaɗen jihohin Najeriya 36 baki ɗayan su.

A ranar Alhamis ce dai Minista Umahi ya gana da wasu gidajen talabijin, inda ya bayyana cewa aikin titin jirgin ƙasa ɗin daga Legas zuwa Kalaba, mai tsawon kilomita 700, zai lashe Naira tiriliyan 15.6. Wato kwatankwacin Dala biliyan 13, kan kowace Dala 1 a Naira 1,200.

Bai daɗe da yin bayanin ba sai Atiku ya maida masa kakkausan raddi, inda ya bayyana cewa an dai buɗe wata kafa ce inda za a riƙa ginar kuɗaɗe ana lodi, ana jida ana gudu da su a ɓoye kawai.

Sannan kuma ya ce an bada aikin kwangilar gina titin jirgin ƙasa ɗin ga kamfanin Gilbert Chagoury, wato Hitech ba tare da bin ƙa’idar gayyatar wasu kamfanoni su zo su kawo tandar neman aikin, kamar yadda doka ta tanadar ba.

“Kasafin jihohin Najeriya 36 na 2024 ma fa Naira tiriliyan 14 ne. Idan ka haɗa da na FCT Abuja, kasafin zai tashi Naira tiriliyan 15.91. Amma kuma saboda ganganci da toshewar tunani, za a gina titin jirgin ƙasa na Naira tiriliyan 15.6, mai nisan kilomita 700.

“Cikin Satumba, 2023, Umahi ya ce Hitech na Gilbert Chagoury zai gina titin. Sai bayan Girbert ya kammala karɓar kuɗaɗen sa a zirga-zirgar jiragen sannan zai damƙa shi a hannun Gwamnatin Tarayya.

“Duk duniya haka kafafen yaɗa labarai su ka buga Umahi ya ce a wancan lokacin, har ma da kafafen yaɗa labarai mallakar Tinubu.

“To don me kuma yanzu Umahi zai zo ya yi mana ƙarya wai Gwamnatin Tarayya za ta bada kaso 15 bisa 100 zuwa 30 bisa 100?”

Atiku kuma ya cika da mamakin yadda ya ce “a cikin kasafin kuɗin 2024 aka lissafa aikin titin jirgin ƙasa na Legas zuwa Fatakwal kan Naira biliyan 500, kamar yadda Majalisa ta amince, amma kuma sai Gwamnatin Tinubu ta fitar da Naira tiriliyan 1.06 kan aikin. Wato an ruɓanya kuɗin kenan har da ɗoriya. To hakan ke faruwa saboda Majalisar Ƙasa ba su aikin da ya wajaba su riƙa yi.” Inji Atiku.

Majiya: Premium Times Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *