Dole China da Turkiyya su hana Iran kai harin ramuwar gayya a Isra'ila — Blinken
- Katsina City News
- 12 Apr, 2024
- 421
Daga Saliadeen Sicey
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira ga takwarorinsa na China, Turkiyya, Saudiyya, da Tarayyar Turai su "hana Iran mayar da martani" bayan Isra'ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira ga takwarorinsa na China, Turkiyya, da sauran ƙasashe su "hana Iran mayar da martani" bayan Isra'ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Damascus
Blinken ya yi magana ta wayar tarho da takwarorinsa na China, Turkiyya, Saudiyya, da Tarayyar Turai inda ya "bayyana musu ƙarara cewa bai kamata a ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya ba sannan ya buƙace su da su yi kira ga Iran kada ta mayar da martani," a kamar yadda kakakin Ma'aikatar Wajen Amurka Matthew Miller ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis.
Kazalika Blinken ya yi magana ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant "domin jaddada goyon bayanmu mai ƙarfi ga Isra'ila kan duk wata barazana da za ta fuskanta," in ji Miller.
Iran ta sha alwashin mayar da martani bayan Isra'ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancinta a Damascus ranar 1 ga watan Afrilun, inda ta kashe zaratan sojoji bakwai na runduna ta musamman ta Revolutionary Guards, cikinsu har da janar-janar guda biyu.