TAHARIN MUTANE DAURI; KABARIN FIR'UNONIN MISIRA.

top-news

A kasa  hoton Makarori ne wata Makarar a cikin wata a jere har guda hudu. Haka Misirawan Dauri suke binne Sarakunansu.
Bayan sun kyafe Gawarsu da Sinadarai da suke hanata rubewa, sai su nannade Gawar da Yadin Alhariri sannan a nannade ta da Guraye, da layun tsafi wanda zai bata kariya har zuwa lokacin da Gangar Jikin zata hadu da Ruhin Ranar karshe.

Bayan Nan sai a saka Gawar a cikin Karamar Makara, wacce za a saka ta a cikin babbarta wadanda duk an Zane Sun da Siddadaru Wanda aka narkar da shi zuwa Hatimin kariya ga Gawar Sarki. Suma sai a rufe su a cikin wata Katuwar Makarar Katako mai dauke da Ado da Zane Zane masu dauke da fasaha da siddabaru daban daban na camfe camfe tsafin Kariya da garkuwa ga Gawar Sarki.

Abin  na karshe shi ne, za a rufe wadannan Makarorin da Wata Katuwar Makara da aka yi da Dutsin Wuta (Granite Rock). Wacce za ta sama Kariya kuma garkuwa ga sauran Makarar da Gawar Fir'auna take ciki. 

Wannan shi ne ake kaiwa binne a makabarta Fir'uonin Misira na Daula ta 18, wacce take.a 'King Valley's ' dausayi ko Kwazazzaben Sarki. Wajen da aka samu Gawarwakin Fir'aunonin Misira da yawa.

Wannan Makarar Fir'auna Tutankhumun ne Kakan Fir'aunan Annabi Musa a.s, wacce aka gano a Shekarar 1922. Haka tsarin yake a Kabarin Fir'auna Yuya da Fir'auna Tuya.

 Wadanda Yan Fashin Makabarta ba su samu damar gano Kabarinsu ba balle su Yashe Dukiyar da take ciki su baddala Tarihinsu. Sai dai wasu Manyan Yan Fashin ne suka gano su suka kwashe suka Kai Karsarsu. Idan kana son ganin wannan Makarorin sai ka garzaya Kasar Manyan Yan Fashin Duniya a birnin London a British Museum.

A view showing how the ancient Egyptians buried kings, 4 coffins inside each oth er to protect the king’s mummy...and these coffins are engraved with special spells - according to his belief - for the return of the soul and the protection of the body of the deceased until he reaches the afterlife. The mummy itself is between the folds of wrapped linen. Dozens of protective amulets skillfully transformed it. Our completed model of the four coffins was found in the tomb of King Tutankhamun and in the tomb of Yuya and Tuya. Here in this model you find this mummy inside a small coffin, then a larger, gilded wooden coffin. Then the large wooden coffin contains the two smaller coffins.. Then all of this was inside a huge granite coffin in the cemetery. The layers of the coffin are shown in the picture on display in the British Museum.

Culled from Ibrahim Daurawa Page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *