TATSUNIYA (5): Labarin Budurwa Marar Tabo
- Katsina City News
- 08 Apr, 2024
- 442
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wata yarinya kyakkyawa, wadda ko tabo daya babu a jikinta.
Shi ke nan, sai ta ce ita fa ba za ta auri wanda yake da tabo ko da aya ne tak a jikinsa ba. Manema wannan ya zo, wancan ya zo, amma duk suna da tabo. Ana nan, sai ga wani saurayi wai shi Dandisheri wanda ba shi da tabo a jikinsa, in ban da wani karami a kan dan yatsansa, shi ma ya je saran itace ne ya yi sartse. Da ya je, sai ta ce ba ta son sa, Ya hakura.
Rannan sai wani maciji ya ji labarin halin wannan budurwa, ya gaya wa abokansa, suka rikida suka zama mutane samari kyawawa, wadanda ba daya daga cikinsu wanda yake da tabo ko daya a jikinsa.
Sai suka je wurinta, ta bincike kowannensu sarai, ta ga babu tabo a jikinsa. Nan take ta ce ta yarda dayansu ya aure ta. Aka taru aka daura aure da dayansu. Shi ke nan ta tattara kayanta suka tafi da amaryarsu.
Da suka je jeji sai suka ce: "Yawwa mun iso gida." Ita ko ta ce: "Ina gidan a nan?" Sai suka ce da ita: “Ai nan ne gidan.
Amarya ta yi zuru-zuru, babu yadda za ta yi domnin ta riga ta auri dayansu. Kuma ga shi sun kai ta dokar daji, inda ba za ta iya komawa gari ba. Daga nan suka saka ta a kogon bishiya, suka rikide macizai suna lasar jikinta har ta zama fara fat, babu kyan gani, kuma abin kyama.
Ana nan kwanci-tashi har ta sami ciki. Bayan wani lokaci mai tsawo, sai tsohon manemin ta Dandisheri suka yi karancin ciyawar akuyarsu, sai ya tafi can cikin kungurmin jeji yana yankan ciyawa.
Sai matar macizai ta hango shi, ta fara rera masa waka tana cewa:
Dandisheri - Dandisherina,
Dandisheri kanin Babati.
Idan ka je gida ka gai da iyata,
Idan ka je gida ka gai da Babati.
Ni mai zabar maza babu tabo,
Ga ni yau a kogon kukati,
Maciji na lasa ta mulai,
Kunama na harbi na mulai."
Sai Dandisheri ya dau waka, ya amsa mata yana cewa:
Ina ruwan Dandisheri,
Daga fari ke aka bai wa ni,
Daga gani sai kika raina ni,
Domin tabon dan yatsana.
Da ya je gida sai ya gaya wa iyayenta halin da take ciki. Da suka ji labari,
sai suka yi shiri domin su je su gani. Da suka je sai suka same ta a cikin kogo. Suka rasa yadda za su fito da ita. Dole aka sare bishiyar, aka fitar da ita, iyayen suka tafi da ita gida.
Daga baya ta haifi ɗa namiji, rabin jikinsa dan mutum, rabi dan maciji.
Da mazanta macizai suka ji ta haifu sai suka kara zama mutane, suka zo
karbar dansu.
Da suka isa gidan, sai danginta suka tona makeken rami, aka shimfida musu tabarma a kai. aka kuma hura wuta a karkashi, aka yi wa dansu wanka aka yi masa kwalliya aka kira su, suka zauna suka karbi dansu suna cikin hira sai su ji 'nyas-nyas, 'sai suka ce: "Kai akwai abin cizo a gidanku?"
Masu gida suka ce: "E wallahi."
Jim kadan sai tabarma da yayin suka kama wuta, su da shimfidar suka
fada cikin wutar.
Yayin da suke konewa sai suka wurgo yaron sama, aka cafe shi, aka Kara wurga musu, haka dai suka yi ta yi har suka kone rumus da su da
dansu.
Da ba domin Gizo ba da na yi muku karya. Kurunkus. Mun ciro wannan Labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman.
Wane Darasin Rayuwa wannan Labarin yake koyarwa...? Mu tattauna