Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta Hana Ayyukan Ɓadala tare da sa Ido ga masu Aikatawa

top-news

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, karkashin Jagorancin babban kwamanda na jihar Katsina Dakta  Aminu Usman (Abu Ammar), ta Ayyana wasu ayyukan baɗala 4 a matsayin haramun tare da daukar matakai akan masu yi.

Ayyukan Baɗalar da suke kara ruruwa kamar wutar daji a jihar Katsina ga matasa wanda Hukumar ta Hana sun hada da.

1. Ayyukan Kide-kide na DJ
2. Sara Suka (Ƙauraye)
3. Wasan Galla
4. Gudanar da bukukuwan Aure da suka  sabawa shari'a

A yunkurin da hukumar Hisbah ta ke na tabbatar da tsaftar Al'umma, ta sake jaddada aniyar ta na sa ido da kuma tabbatar da bin doka a fadin jihar.

Hukumar Hisbah ta hada kai da jami’an tsaro na jihar Katsina, ta yi alkawarin daukar kwararan matakai na kawar da duk wata barna da rashin da’a a jihar Katsina. Hukumar ta bukaci iyaye, malaman addinin Islama, da shugabannin al'umma da su kasance a faɗake tare da ba da goyon baya ga kokarin jagoranci da kula da matasa.

Sa hannu:
Mallam Nafi'u M. Aƙilu
Jami'in Hulda da Jama'a
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina
- Afrilu 7, 2024 -

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ayuba adamu tsiga

Allah sarki rayuwa mahakurci mawadaci .lokaci maisauyawa yadda ubangiji yaso dacan abaya yan hisbah sukadai suke fadi tashi suyi kidan su suyi rawar su wajen yaki da badala.dayawan lokuta muna fita patrol musha dakyar agun dj wani lokacin mukai samame gidan badala abimu da jifa zagi ta uwa ta uba.munaji muna gani wasu abubuwan dole muke hakuri babu yanda zamuyi dan bamu da uwa agindin murhu amma yau anwayi gari kungiyar hisbah tazama hukuma munzama masu yanci munada doka da oder gaskiya musulunci yaci gajiya irin wadda bai taba ciba ajihar katsina allah mungode ma daka bamu da mai ido jajirtaccen gwamna ma'abocin addini mai kishin musulunci wanda yakeyi dan al'uma bawai dan kansaba.ya ubangiji kayimasa jagora aduk lamuran sa kabashi kariya daga dukkan sharri commander general munayima fatan alkhairi kuma munama kyakykyawan zato ya allah yabaka ikon rikewa da amana yabaka kariya aduk lamuran ka,bello abubakar guga commander bakori divs allah yabaka nasara a irin gwagwar mayar dakakeyi da komai naka