Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta Ayyana Wasu Ayyukan Barna a Matsayin Haramun a Hukumance, tare da sanya Ido ga masu yi.

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

A ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu 2024 Hukumar ta Ayyana Wasan Gala, Kauranci (Sara suka) Kaɗe-kaɗen DJ, tare da soke shugabancin Kungiyar Hisbah da ba ta gwamnati ba.

Haka Zalika, Hukumar ta Haramta Yin wasu Al'adu a wajen Bukukuwa ba tare da Izini ba a rubuce, Izinin kuma zai biyo bayan aike da sako da bayyanawa hukumar yanda za'a gudanar da Al'adun bukukuwan don tantance wanda bai sabawa Shari'a da hankali ba.

Wadannan bayanai duka sun fito ne daga bakin Babban Kwamandan ta na jihar Katsina, Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) a wajen taron wayar da kai da karama juna sani da hukumar ta shirya a bangarorin kungiyoyin Addinin musulunci da zasu yi aiki kafada da kafada da hukumar don yaki da Baɗala a jihar Katsina.

Taron da aka gabatar a babban dakin taro na ma'aikatar Kananan Hukumomin jihar Katsina ya samu halartar Gwamnan jihar Katsina wanda mataimakin sa Farooq Lawal Jobe ya wakilta, inda ya gabatar da jawabi a madadin Gwamnan jihar Katsina.

Tare da jawabin kwarin gwiwa daga bakin Babban Alkalin Alkalai na jihar Katsina, mai shari'a musa Danladi Abubakar, wanda ya bayyana cewa sunyi Nazarin Dokokin da suka kafa hukumar Hisbah babu inda tayi karo da Dokokin kasa ko na jiha wanda zai iya haddasa rashin jituwa tsakanin Al'umma.

Don haka Babban Alkalin ya bada Shawara kafa Kotun Tafi da gidan ka don gaggawar yanke hukumci akan duk wanda aka kama ya saba Doka, yace "idan akai haka zai sanya dole mutane su zamo masu da'a.

Manyan Malamai sun gabatar da Kasida akan Minene Hisbah, Asalinta da yanda yakama Dan Hisbah ya zama. Tare da Addu'o,i na fatan Alheri ga taron da Mahalarta taron da suka hada da Kungiyoyin Darika, Izala, Kur'aniyun da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ayuba Adamu

hisbah sojojin musulunci, Hakika ita wannan runduna bataliya ce mai umarni da kyakykyawa, hani da mummuna ta hanyar fadakarwa da nasiha dakuma tsawatarwa, domin samun tsarka-kakkiyar al'umma mai cike da tsoron Allah dake wanzuwa Adoron kasa, zahiri su wadannan jami'ai sunawa addinin Allah hidima ne baki daya basu da wani bambanci na akida akan 'yan uwa musulmai.kamar yanda addinin ubangiji yake guda daya tak islam haka kawunan wadannan jami'ai yake guri daya ya ubangiji ka tsarkake mana zukatammu, kayi mana jagoranci,kayafe mana kura kurammu ya ubangiji kajikan magabatammu kasamucika da imani,