ZAMFARA BATA CI WANI SABON BASHI BA ....
- Katsina City News
- 01 Apr, 2024
- 343
@ Katsina Times
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta ciwo bashin kuɗi Naira Biliyan 14.26 ba, sai dai wani ɓangare na bashin Naira Biliyan 20 wanda gwamnatin da ta shuɗe ta ciwo.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ba a ciyo bashin gida ko waje ba tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal.
“Muna so mu fayyace wa Ofishin Kula da Basussuka (DMO), cewa Gwamnatin Zamfara ba ta ciyo bashin Naira Biliyan 14.26 ba.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ba ta taɓa neman lamuni ko tuntuɓar majalisar jiha ko ta ƙasa domin neman wannan buƙata ba.
“Yana da kyau a lura da cewa Gwamnatin Jihar Zamfara da ta shuɗe ta ciwo bashin naira biliyan 20, amma ba ta karɓi duka kuɗin ba.
“Gwamnatin da ta gaba ta karɓi Naira Biliyan 4 daga cikin bashin Naira Biliyan 20 da gwamnatin Zamfara ta nema don aikin filin jirgin sama, duk da ya ke ba a yi amfani da kuɗin ba.
“Lokacin da muka shiga ofis, mun samu cewa ba zai yiwu a bi yarjejeniyar biyan bashin, b tare da an jawo wa jihar nan gagarumar asara ba.
“Ragowar Naira Biliyan 16 daga cikin Naira Biliyan 20, wanda gwamnatin da ta shuɗe ta ranto, shi ne Naira Biliyan 14.26 da ofishin kula da bashi DMO ya ambata. Kimar sa ta ragu saboda hauhawar farashi.
“Wannan ragowar, wanda yana nan a asusun gwamnati, ba a yi amfani da shi ba, za a yi amfani da shi ne a aikin filin jirgin saman."
SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara
1ga Aprilun 2024